Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana harbin da aka akaiwa jerin gwanon motocin Shugaban Ƙasa a kusa Dutsinma ta Jihar Katsina a matsayin abun takaici.
Jerin gwanon motocin dai na dauke da ƴan gaba ne na Shugaba Buhari da suka haɗa da jami’an tsaro, masu tsare-tsare da masu yaɗa labarai waɗanda ke shigewa gaba kafin Shugaba Buhari ya biyo baya a tafiyarsa zuwa Daura bikin sallah.
Wannan dai ya bayyana ne a jawabin da Mai Temakawa Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai, Garba Shehu ya saki a jiya Talata da yamma.
Garba Shehu ya kuma yabawa ƴan gaban bisa magance matsalar harin ƴan bindigar.
Ya ce, “Masu kai harin sun bude wuta ne kan jerin gwanon ta hanyar kwantob ɓauna, amma masu raka jerin gwanon da suka haɗa da sojoji, jami’an tsaron farin kaya da ƴansanda suka daƙile harin.
“Mutane biyu daga cikin jerin gwanon suna karɓar magani kan ƙananan raunuka da suka samu. Duk sauran ma’aikatan da motocin sun isa Daura lafiya.”