For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ƴan Boko Haram 64 Ne Suka Tsere Daga Kuje Bayan Kai Hari

Dukkanin waɗanda ake zargin kwamandojin ƙungiyar Boko Haram ne su su 64 sun tsere a yayin harin da aka kai gidan yarin Kuje da ke Abuja a daren ranar Talata.

Rahotanni sun fursunoni huɗu ne tare da wani jami’in tsaro na hukumar NSCDC suka rasa rayukansu a lokacin harin.

Ƙungiyar ƴan ta’adda ta Islamic State of West Africa Province, ISWAP, a daren jiya Laraba, sun amsa cewa sune suka kai harin.

Ministan Tsaro, Maj. Gen. Bashir Magashi, ya ce salon harin da aka kai ya nuna cewa ƴan Boko Haram ne suka kitsa shi.

Ya ƙara da cewa, ƴan ta’addar masu tarin yawa, sun kai harin ne da misalin ƙarfe 10:25 na dare, inda jami’an tsaron da ke gadin gidan yarin sukai iya bakin ƙoƙarinsu wajen yaƙarsu.

Ya ce, “Bincike ya nuna cewa, ƴan ƙungiya ɗaya ne – Boko Haram. Kuma dukkanninsu da ke cikin gidan yarin sun tsere.

Tsohon Ministan Cikin Gida, Janar Abdurrahman Dambazau ya bayyana jiya da daddare a wani shiri na talabijin cewa, da yawa daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar Boko Haram suna cikin gidan yarin tsawon shekaru 10.

Janar Dambazau ya ce, dole ne a zargi masu ruwa da tsaki a harkar tsaron gidan yarin da sakaci kan lamarin.

Ya kuma ƙalubalanci jami’an tsaron da cewa, tun da an samu bayanan sirri na cewar za a kai harin, kamata yai a daƙileshi tun kafin faruwarsa.

Harin na gidan yarin Kuje dai, ya zo ne a rana ɗaya da harin da aka kai wa jerin gwanon motocin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a lokacin da masu temaka masa suka wuce gaba domin shirya zuwansa Daura bikin babbar sallah.

Comments
Loading...