Baba Sayinna Goni Mukhtar daga Jihar Borno da Haulatu Aminu Ishak daga Jihar Zamfara ne suka zama gwarazan gasar karatun Alkur’ani ta Kasa ta 36 wadda aka gudanar a Bauchi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ya rawaito cewa, ƴan takarar sun lashe gasar ne a mataki na farko wato haddar izifi 60 da tafsiri a ɓangaren maza da kuma mata.
Gasar da aka ɗebe mako guda ana gudanarwa, wadda Gidauniyar Musabaqar Karatun Al-Qur’ani a Najeriya kuma Cibiyar Nazarin Ilimin Musulunci ta Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sokoto haɗin gwiwa da Gwamnatin Jihar Bauchi suka shirya an kammalata ne a jiya Asabar.
Ƴan takarkaru 328 ne da suka fito daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja suka fafata a ajuzuwa 6 na gasar.
Ajuzuwan sun haɗa da haddar izifi sittin da tafsiri da tajwidi; haddar izifi sittin da tajwidi; haddar izifi 40; haddar izifi 20; haddar izifi 10 da tangimi da kuma haddar izifi 2 na Al-Qur’ani mai girma.
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad ya baiwa gwarazan biyu kyautar naira miliyan 3 kowannesu saboda ƙwazon da suka nuna a yayin gasar.
Haka kuma, Musa Ahmad Musa da Maryam Habibu Abubakar ƴan Jihohin Borno da Zamfara suma sun sami kyautar naira miliyan 2 kowannesu bisa nasarar da suka samu a aji na biyu na haddar izifi sittin da tajwidi.
Sauran ƴan takarar da suka samu nasarar zuwa 1 zuwa 5 duk sun sami kyaututtuka daban-daban.
Jihohin Da Suka Sami Nasara A Kowanne Aji
Izifi 2 Hadda (Maza)
5- Enugu
4- Abia
3- Imo
2- Edo
1- Cross River
Izifi 2 Hadda (Mata)
5- Imo
4- Bayelsa
3- Enugy
2- Edo
1- Anambra
Izifi 10 da Tangimi (Maza)
5- Zamfara
4- Jigawa
3- Kogi
2- Borno
1 Kano
Izifi 10 da Tangimi (Mata)
5- Gombe
4- Zamfara
3- FCT Abuja
2- Jigawa
1- Borno
Izifi 20 Hadda (Maza)
5- Kaduna
4- Jigawa
3- Kebbi
2- Kwara
1 Sokoto
Izifi 20 Hadda (Mata)
5- Kwara
4- Kaduna
3- Taraba
2- Borno
1 FCT Abuja
Izifi 40 Hadda (Maza)
5- FCT Abuja
4- Kaduna
3- Zamfara
2- Katsina
1- Borno
Izifi 40 Hadda (Mata)
5- Kaduna
4- Imo
3- Adamawa
2- Nasarawa
1- Kano
Izifi 60 Hadda (Maza)
5- Kogi
4- Yobe
3- Kebbi
2- Zamfara
1- Borno
Izifi 60 Hadda (Mata)
5- Kaduna
4- Jigawa
3- Oyo
2- Bauchi
1- Zamfara
Izifi 60 da Tafsiri (Maza)
5- Jigawa
4- Zamfara
3- Bauchi
2- Niger
1- Borno
Izifi 60 da Tafsiri (Mata)
5- Yobe
4- Gombe
3- Fct Abuja
2- Katsina
1- Zamfara
Da yake jawabi a wajen taron rufe gasar, Shugaban Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sokoto, kuma Shugaban Gidauniyar Musabaqar Karatun Al-Qur’ani, Farfesa Lawal Bilbis ya yi kira ga ƴan takarkarun da su yi kyakkyawan amfani da ilimin da suka samu.
Manyan baƙin da suka sami halartar taron rufe gasar sun haɗa da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar lll, Sarakunan Bauchi, Katagum, Dass, Jama’are, Misau da Ningi da kuma malaman addinin Musulunci da dama.