Ƴan ta’adda da ke kusan kowanne yanki a Najeriya sun kai hari kan sansanin sojoji 16 cikin watanni 18 da suka gabata, abun da ke nuni da cewa, sojoji na cikin takura da kuma buƙatar sake shiri domin magance ɓatagarin, kare jami’ai da kuma kawo karshen matsalar tsaro.
Binciken da SUNDAY PUNCH ta yi ya nuna cewa, yayin da wasu hare-haren suka kai ga kisan wasu sojojin, wasu kuma an magancesu tare da kashe ƴan ta’addar.
An kuma gano cewa, cikin ƴan watannin da suka gabatan, kusan sojoji 800 ne aka kashe ɓangarori da daban-daban na ƙasar.
Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari a ranar Juma’ar da ta gabata, ya bayyana cewa ba za a aminta da yawan hare-haren da ke faruwa a ƙasar ba, inda ya zargi wasu ƴan ƙasashen waje da iza wutar matsalar tsaron da ke addabar ƙasar.
Hare-Hare A Kan Sojoji
Binciken da SUNDAY PUNCH ta yi ya nuna cewa, hare-haren da aka kai sansanin sojojin sun faru ne a yankin Arewacin ƙasar.
A shekarar nan ta 2022, an samu manyan hare-hare a sansani guda 6, waɗanda suka faru a Jihohin Borno, Katsina, Kaduna, Taraba da kuma Jihar Niger.
Waɗannan daban suke da da sauran hare-haren da aka kaiwa sojojin, waɗanda suka haɗa da kwanton ɓauna daban-daban, hari a kan jerin gwanon motocinsu, sannan da kuma na kwanakwanan nan wanda aka kai kan wajen binciken ababan hawa na Zuma Rock a ranar 28 ga watan Yuli, inda har aka kashe soja guda ɗaya.
A wasu hare-haren kan sansanin sojojin, ƴan ta’addar sun kai hari kan sansanin soja a garin Sarkin Pawa da ke Ƙaramar Hukumar Munya a Jihar Niger a ranar 18 ga watan Yuli, 2022.
Gwamnan Jihar Niger, Abubakar Sani Bello ne ya bayyana hakan, inda ya ce sojoji sun samu nasarar daƙile harin yana mai cewa ba a samu mutuwa ba a harin daga ɓangaren sojoji.
A ranar 10 ga watan Mayu, wasu ƴan ta’adda da akai zargin ƴan ƙungiyar ISWAP ne sun kai hari kan sansanin 6th Brigade na sojoji da ke Jalingo a Jihar Taraba.
An ce sun jefa bom ne zuwa sansanin da misalin ƙarfe 8:44 na dare, sai dai kuma ba a samu hasarar rai ko rauni ba a sanadiyyar hakan.
Haka kuma a ranar 4 ga watan Afrilu, waɗansu ƴan ta’addar da akai zargin ƴan Ansaru ne sun kai hari sansanin sojoji da ke Polewire kan titin Kaduna-Birnin Gwari a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna, wanda aka harbe sojoji 11 har lahira yayin da kuma wasu 19 suka sami raunuka.
Ƴan ta’addar waɗanda sukai amfani da bindigar harba gurneti, sun kuma kashe ƴan bijilanti guda 3 tare da jiwa biyu raunuka.
A makamancin hakan, an rawaito cewa mayaƙan ISWAP sun kai hari kan sansanin sojoji na ƙasa da ƙasa da ke Doron Baga, a Ƙaramar Hukumar Kukawa ta jihar Borno a ranar 19 ga watan Maris.
Su ma sojoji hadin guiwa da rundunar Operation Hadin Kai, sun yi nasarar daƙile harin tare da kashe wasu ƴan ta’addar.
Rahotanni sun ce ƴan ta’addar sun je kai harin ne da motocin bindiga guda biyar da kuma gurneti da yawa sai dai kuma sojojin sun ci nasara bayan ɗebe kimanin awa biyu suna musayar harbe-harbe da ƴan ta’addar.
Haka kuma rahotanni sun nuna cewa, a ranar 21 ga watan Janairu ƴan ta’adda sun mamayi sansanin sojoji da ke cikin Makarantar Sakandiren Gwamnati ta Jeka ka Dawo da ke Shinfada, a Ƙaramar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina.
Wani soja da jami’in Civil Defence sun rasa rayukansu a sanadiyyar harin.
Mai magana da yawun hukumar Civil Defence, Muhammed Abdara ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga ƴanjarida.
A shekarar 2021, rahotanni sun nuna cewa, aƙalla hare-hare 11 aka kai a kan sansanin sojoji da ke yankin Arewa, yayin da sojojin suka ci nasarar daƙile wasu daga cikinsu.
A watan Janairun 2021, mayaƙan Boko Haram da ISWAP sun kai hari sansanin New Marte a Jihar Borno.
Rundunar Sojojin ta bayyanawa ƴanjarida cewa ta daƙile harin ta hanyar haɗin gwiwa da rundunar Operation Lafiya Dole, da kuma rundunar Sojojin Sama.
A watan Fabrairu, a wani waje marar tazara da garin Dikwa a Jihar Borno, ƴan ƙungiyar Boko Haram sun kai hari kan wajen ya da zangon sojoji da ke yankin.
Rahotanni sun nuna cewa, an kai harin ne domin a samu damar kaiwa ga sansanin Majalissar Ɗinkin Duniya da kuma kwace garin, sai dai kuma sojojin rundunar Operation Lafiya Dole da sauran sojoji sun daƙile harin.
Sojojin ba su bayyana adadin waɗanda suka rasu ko suka ji rauni a harin ba.
Mai magana da yawun sojoji, Brig. Gen. Mohammed Yerima, ya bayyana cewa, ƴan ta’addar sun shiga garin da motoci ɗauke da bindigu da kuma babura sai dai kuma sojojin sun samu nasarar daƙile su.
A watan Afrilu na 2021, sojoji sun tabbatar da cewa sansaninsu da ke Mainok a Jihar Borno ya fuskanci harin ƴan ta’addar ISWAP.
Ƴan ta’addar sun fara da yiwa sojojin kwanton ɓauna ne a lokacin da suke yin rakiyar makamai zuwa cikin sansanin na Mainok.
Daga baya kuma suka kaiwa sansanin hari, inda aka rawaito cewa sun kashe sojoji da dama ciki har da kwamandansu wanda ke da mukamin lieutenant colonel.
An rawaito cewa sun dauke motocin kare kai daga kwanton ɓauna guda biyu sannan daga baya suka ci karfin sojojin suka kuma kone motocin sojojin da dama.
Sai dai kuma Yarima ya ce, harin hari ne daga ɓangarori da dama kuma ya jawo asarar ran ma’aikaci guda ɗaya da kuma sojoji guda shida, yayinda kuma sojoji shida suka sami raunuka.
A watan Mayu na 2021, wasu da ake zargin ƴan Boko Haram ne sun kai hari sansanin sojoji na ƙauyen Ajiri da ke Ƙaramar Hukumar Mafa ta Jihar Borno.
An rawaito cewa, ƴan ta’addar sun ƙwacewa sojojin makamansu a lokacin da suka kai harin.
Mafa ƙaramar hukuma ce da aka killace ƴan gudun hijira waɗanda suka bar gidajensu saboda matsalar tsaro a jihar.
Haka kuma sojojin sun kai hari kan makarantar horar da sojoji ta Nigeria Defence Academy da ke Afaka a Kaduna a watan Agusta na shekarar 2021.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, ƴan ta’addar sun kashe sojoji biyu yayin da suka yi garkuwa da wani Major mai suna Christopher Datung, sai kuma soja ɗaya da aka kwantar a asibiti dalilin harin.
A ranar 12 ga watan Satumba na shekarar, ƴan ta’adda sun kai hari kan sansanin Ƴan Gaba da ke Mutumji, a Ƙaramar Hukumar Ɗansadau da ke Jihar Zamfara, inda suka kashe jami’an tsaro aƙalla 12.
Tara a cikinsu sojojin sama ne, biyu ƴansanda da kuma sojan ƙasa guda ɗaya inda kuma aka samu waɗanda suka ji raunuka a ɓangaren ƴan ta’addar da kuma jami’an tsaron.
A ranar 26 ga watan Satumbar dai kuma aka samu rahoton cewa, wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kashe wasu mambobin rundunar haɗin gwiwa lokacin da suka kai hari kan wajen ya da zangon sojoji na Burkusuma da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.
Harin da aka kai da sanyi safiya, mutanen ƙauyen ne da suka tsere zuwa babban birnin jihar suka sanar da manema labarai.
Kwamishinan Harkokin Tsaro na jihar, Col. Garba Moyi (mai ritaya), wanda shi ma ya tabbatar da afkuwar harin a kan sojojin, ya ce, bai da masaniyar yawan waɗanda abun ya rutsa da su.
An rawaito cewa, ƴan ta’addar sun ci ƙarfin sansanin inda suka ƙone motocin sintiri tare da sace kayan abinci.
Jaridu sun rawaito cewa, ƴan ta’addar ISWAP sun kai hari kan sansanin Majalissar Ɗinkin Duniya a Rann a dai wannan watan.
Sun farmaki sansanin ne wanda ke kan iyakar Najeriya da Kamaru domin su ƙwace iko da garin da ke kan iyakar.
Wata majiyar tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta rawaito cewa, wani soja da kuma wani ɗan sa kai da ke aiki da wata hukumar wata ƙasar waje sun rasa rayukansu a harin.
A lokacin da rundunar sojoji take tabbatar da aukuwar harin ta ce, jami’anta sun daƙile harin ba tare da ƴan ta’addar sun samu nasarar korar sojojin daga sansanin ba.
A ranar 8 ga watan Nuwamba na 2021 ma, wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar ISWAP ne sun farmaki sansanin sojoji da ke ƙauyen Tamsukawu a Ƙaramar Hukumar Kiaga ta Jihar Borno.
Kwamandan Sashi na 3 na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Fararen Hula, Modu Fannami ya faɗawa ƴanjarida cewa, ƴan sojojin da ke sansanin sun fafata da ƴan ta’addar, amma bai faɗi adadin waɗanda abun ya rutsa da su ba a kowanne ɓangare.
A dai watan na Nuwamban shekarar 2021, an rawaito cewa ƴan ISWAP sun kashe wani birgediya janar lokacin da suka kai farmaki kan sansanin sojoji da ke Askira a Ƙaramar Hukumar Uba a Jihar Borno.
An kuma rawaito cewa wasu sojoji uku sun rasa ransu a Bulgama, ƴan kilomitoci daga garin na Askira.
A watan Disamba, mambobin ƙungiyar ISWAP sun mamayi sansanin sojoji da ke Rann a Ƙaramar Hukumar Kala Balge da ke Jihar Borno.
An rawaito cewa, sojoji shida sun mutu a harin yayin da a ɓangaren ƴan ta’addar guda 20 suka mutu a ƙoƙarinsu na ƙwace sansanin.
Akwai matuƙar abun dubawa kan yawaitar kai hare-hare kan sansani da kuma wajajen ya da zangon sojoji da ma sauran gurare a sansan Najeriya.