Wani Likitan mai suna Dr. Dave Okorafor, a shafinsa na Facebook, jiya Lahadi da yamma, ya rubuta alhinin kisan direbansa wanda wasu ƴanbindiga suka kashe a Onitsha ta Jihar Anambra.
Ya rubuta cewa, a jiya duk da kasancewar ta Lahadi amma ana kashe mutane a Onitsha, ko me yasa hakan? Ko jiyanma ana bukatar mutane su zauna a gidajensu ne?
A dai cikin rubutun nasa ne ya rubuta cewa, ƴanbindiga sun harba tare da kashe direbansa a tollgate na Onitsha da tsakar rana.
Ya kara da cewa, lokacin da yake rubutun ya nuna kimanin awanni biyu kenan da faruwar lamarin amma babu wani jami’in gwamnati da ya je wajen da abun ya faru.
Ya kuma ce, wasu ƙarin mutane biyu ma sun gamu da ajalinsu tare da direban nasa, kuma har lokacin rubutun nasa gawarwakinsu na wajen.
Da yake jaddada ƙorafinsa game da ƙin zuwan ƴansanda wajen, Okorafor ya ce, an sanar da ƴansanda da ke ofishinsu na Ogbunike, amma sai suka ce lokaci ya ƙure na zuwa tollgate din Onitsha.
Sai dai suka ce, sun amince mana da mu ɗau gawar direba na zuwa wajen ajjiye gawarwaki.