For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ɗan Majalissar Tarayya Ya Fice Daga APC Ya Koma PDP

Ɗan Majalissar Wakilai mai wakiltar Mazaɓar Majalissar Wakilai ta Birnin Kebbi, Kalgo da Bunza, Bello Yakub Rilisco a ranar jiya Alhamis, ya sanar da fitarsa daga jam’iyyar APC inda ya koma jam’iyyar PDP a jihar Kebbi.

Da yake tabbatar da ficewar, babban mai temaka masa a harkokin majalissa wadanda suka shafi siyasa, Hussaini Shehu ya ce, Ɗan Majalissar ya fice daga jam’iyyar APC ne saboda gazawarta wajen cika alkawuran da tai ga ƴaƴanta wadanda suka temaka mata ta kai ga nasara.

Ya baiyana cewa, bayan sauran ƴan kishin jam’iyya, Hon. Bello a matsayinsa na ɗan Majalissar Tarayya shima ba a kula shi a harkokin tafiyar da jam’iyyar.

Ya yi zargin cewa, jam’iyyar APC a jihar Kebbi na bin ra’ayi ɗaya duk kuwa da sauran ra’ayoyin ƴan jam’iyyar, abin da ya jawo hatsaniya da rarrabuwar kai a tsakanin ƴan jam’iyyar a jihar.

Ya kara da cewa, mai gidan nasa bai taɓa samun wani bayani ko a gaiyace shi ba kan zaɓen shugabannin jam’iyya a mazaɓu, ƙananan hukumomi, da kuma jiha, abin da ya saɓawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC wanda ya ce dole ne a dama da dukkanin wani zaɓaɓɓe ɗan jam’iyya a al’amuran da suka shafi mazaɓarsa.

Ya kuma yi kira da magoya bayansa da su zauna lafiya tare da bin doka, sannan kuma ya yi alkawarin ci gaba da yin aiyukan alkhairin da yakewa al’ummarsa da ma ƙasa gaba ɗaya.

Ya kuma yabe su bisa kasancewarsu cikin waɗanda suka yanke hukuncin ficewa daga jam’iyyar ta APC.

(VANGUARD)

Comments
Loading...