Kusan mutane 50 ne aka rawaito cewa, ƴan bindiga sun yi garkuwa da su bayan sun kaiwa motocinsu hari a kan titin Sokoto zuwa Gusau.
Matafiyan dai na dawowa ne daga garin Tambuwal da ke Jihar Sokoto a ranar Asabar da ta gabata da yamma lokacin da maharan suka farmake su.
Ƴan bindigar sun kai harin ne kan doguwar mota coaster da wata guda ɗaya da kuma ƙananan motoci guda biyu.
Lawal Ja’o, ɗaya ne daga cikin mutanen cikin motocin wanda ya tsira, ya ce, an kai harin ne a daidai garin Dogon Awo da ke Ƙaramar Hukumar Tureta a Jihar Sokoto.
Ya baiyana cewa, sun fara jin harbe-harben bindiga ne kafin daga bisani maharan su farmaki mota ta farko.
Ya ƙara da cewa, kusan mutane 50 ne aka tafi da su, inda ya ce, suna jin kururuwar ƴan uwan nasu amma babu abin da zasu iya yi.
Ja’o ya ce, ba su sami damar fitowa daga inda suka ɓuya ba har sai bayan da jami’an tsaro suka isa wajen.
Wani fasinja da ya shaida faruwar lamarin mai suna, Jabiru Shehu ya ce, mun ga motoci huɗu babu mutane a ciki sai jakankuna da kuma wayoyin wasunsu, inda ya ce yana wajen lokacin da ƴansanda daga Tureta suka iso wajen.
Mai magana da yawun ƴansanda a Jihar Sokoto, Sunusi Abubakar ya ce, rundunar ƴansanda ta jiha ba ta sami labarin faruwar lamarin ba, inda ya ce, amma za a tuntuɓi ofishin ƴansanda na yankin da abin ya faru domin jin ba’asin abin.