Kashe-kashe da satar mutane da wawushe dukiya ya talasta wa mutum sama da mutum 200,000 daga Najeriya tsallakawa zuwa Nijar.
Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ƴan Najeriya 11,500 hare-haren ƴan ibndiga daga yankin Sokoto suka tsallaka yankin Tawa na Nijar a watan Nuwamba.
Rahoton hukumar ya ce yawancinsu mata ne da yara ƙanana da suka samu mafaka a ƙauyuka 26 na kan iyaka a Nijar.
Hukumar ta ce ƴan Najeriya 57,000 ke yankin Maradi, mutum 15,000 a yankin Tawa.
Daga: BBC Hausa