Shugaban Shirin Kula da Cututtukan AIDS da STDs na Ƙasa, Dr. Adebobola Bashorun ya ce, a ƙalla mutane miliyan 19 ne ke fama da ciwon hanta a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne jiya Juma’a a Abuja lokacin da yake jawabi ga mahalarta taron da Ma’aikatar Lafiya ta shirya kan tunawa da Ranar Ciwon Hanta ta Duniya.
Taken ranar na bana shine “Hanta Ɗaya Rayuwa Ɗaya.”
Labari Mai Alaƙa: Ma’aikatan Lafiya Zasu Shiga Yajin Aikin Da NLC Ta Shirya Shiga Ranar Laraba
Ciwon hanta dai wani ciwo ne da ke lalata naman hanta, kuma yana da kaloli biyar da suka haɗa da A, B, C, D, da kuma E.
Bashorun ya ce, iya kaso 60 cikin 100 na ƴan Najeriya ne suka san batun ciwon hanta, su ma kuma a cikinsu, kaso 50 ba su san ya lafiyar hantarsu yake ba.
Ya ce, wannan matsalar ce ta sa ake da buƙatar ƙara wayar da kan al’umma da kuma samar da hanyoyin samun gwaji domin sanin halin da mutum yake ciki.
Ya ƙara da cewa, ana ci gaba da yin rigakafin cutar da yara, sannan kuma an tanadar da wata rigakafin domin manya don kare su daga kamuwa da cutar mai kalar B.
