For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ƴan Najeriya Na Nadamar Cin Zaɓen Tinubu Da APC, In Ji PDP

Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, reshen Jihar Ondo, a jiya Talata, ta bayyana matsayarta kan yanayin wahalar rayuwar da ƴan Najeriya ke sha, wadda jam’iyyar ta bayyana a matsayin abun da aka ƙaƙabawa ƴan Najeriya ta hanyar tallata Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ta yi.

Babbar jam’iyyar adawar ta bayyana cewar da yawa cikin waɗanda suka goyi bayan jam’iyyar APC yanzu haka na nadamar hukuncin da suka yi na rashin lissafi wanda ya sa su cikin da-na-sani.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na PDP a Jihar Ondo, Kennedy Peretei ne ya bayyana hakan lokacin da yake mayar da martani kan maganar da Shugaban APC na jihar, Ade Adetimehin yai na cewar, jam’iyyar PDP ta zama tsohon yayi.

KARANTA WANNAN: Mazaɓun Sanatoci 6 Da Ba Su Taɓa Yin Gwamna Ba Tun 1999

Kennedy ya ce maimakon shugaban APCn yai waɗannan maganganu, kamata yai ya bai wa ƴan Najeriya haƙuri a madadin APC kan irin matsatsi da wahalar da suka sa su a ciki.

Ya ce babu buƙatar muhawara da Ade na APC kan surutan da yai, inda ya ce, shi Ade shine kaɗai wataƙil da bai san cewar mutanen Jihar Ondo suna sane da gwamnatin rashin tausayi da ta jefa su cikin mawuyacin hali tsawon shekaru takwas, musamman cire musu tallafin mai da ta yi.

Comments
Loading...