Ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce, saboda lalacewar dukkanin bangarorin cigaban tattalin arzikin Najeriya ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar APC, ƴan Najeriya zasu sakawa jam’iyyar mai mulki da abin da tai musu wajen kawar da ita a shekarar 2023.
Atiku Abubakar, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, ya faɗi hakan ne a shafinsa na Twitter jiya Litinin lokacin da yake kokawa kan wahalhalun da ƴan Najeriya ke shiga a zamanin shugabancin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Atiku ya yi nuni da cewa, matsalolin da ke addabar Najeriya, wasu shaidu ne da ke nuni na gazawar ƙasar a matsayinta na ƙasa.
A rubutun, Atiku ya ce, “Duhun da ya lulluɓe ƙasa cikin ƴan kwanakin nan saboda rugujewar hanyar samar da wutar lantarkin ƙasar, wani abu ne da ke nuni da gazawar ƙasa: lalacewar haɗin kan ƙasa, rugujewar tattalin arziki, rugujewar harkar ilimi, rugujewar walwala, ƙauracewar darajanta ɗan Adam da martaba shi.
“Abin da nake sa rai shine, ƴan Najeriya zasu rusa jam’iyyar APC kamar yanda ta rusa su, ta hanyar zaɓe, sannan su zaɓi tafarki mai kyau da zai samar da sabuwar Najeriyar da muke fata, mai hadin kai da nutsuwa, ci gaba da kuma damammaki masu yawa, mai cike da tsaro kuma wadda ake damawa da kowa. Idan muka dunkule guri ɗaya, zamu ci nasara.