For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ƴanbindiga Sun Kama Mutum 22 A Wani Sabon Hari A Kaduna

A wasu hare-hare daban-daban da aka kai, ƴan bindiga sun sace mutum 19 a unguwar Mani kusa da wani kamfani a Mazaɓar Rido da ke Ƙaramar Hukumar Chikun da kuma yankin Danhonu II Millennium City a Kaduna.

A garin na Mani, ƴan bindigar sun sace wata mata tare da ƴaƴanta uku a safiyar ranar Alhamis.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa ƴan bindigar sun sace ƴan’uwansa shida daga cikin wadanda aka tafi da su zuwa daji.

Ya ce, “Mutane 19 aka sace daga gidaje uku a ƙauyen Mani da ke gaban kamfanin Indomie a Maɓar Rido ta Ƙaramar Hukumar Chikun a safiyar yau (Alhamis). Na san sunayen ƴan’uwana da abin ya shafa. Muna cikin damuwa, musamman ganin har yanzu ba mu ji komai daga masu garkuwar ba. Ciki har da wata uwa mai shayarwa tare da ƴaƴanta hudu, matasa, da jariri.”

Ya yi kira ga hukumomi da su kawo ɗauki ga waɗanda aka sace.

A wani harin makamancin haka, bayan watanni biyu da sace wasu ƴan jarida a Dan Honu II, New Millennium City cikin Ƙaramar Hukumar Chikun, ƴanbindiga sun sake kai hari a daren Laraba inda suka sace wata uwa da ƴaƴanta uku.

Wata majiyar ta ce ƴan bindigar sun kai hari gidan Mista Mutiu Adeleke inda suka sace matarsa da ƴaƴansu uku, suka bar shi shi kaɗai.

Bayan da ƴan bindigar suka yi harbe-harbe da yawa ne suka tsorata kowa suka tafi da mutanen, sai dai daga baya an samu rahoton cewa matar da ba ta iya cigaba da tafiya da su ba, sun barta a cikin daji, inda ta dawo gida, amma suka tafi da ƴaƴan nata.

Comments
Loading...