Wasu ƴanbindiga sun cinnawa motar sintiri ta ƴansanda wuta bayan sun harbe ƴansanda biyu har lahira, abin da ya sa mutane tserewa zuwa cikin dazuka domin tsira da ransu a jiya Lahadi.
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a kan titin Ughelli zuwa Asaba a daidai shataletalen Oleh.
Sai dai ba a samu tabbacin ko ƴanbindigar sun saci bindigogin ƴansandan ba, amma dai lamarin ya jawo gagarumin tashin hankali a yankin, abin da ya kai matafiya na tsoron bin hanyar.
Ƴnsandan da aka kashe na aiki ne da rundunar ƴansanda ta Dragon Patrol a Jihar ta Delta.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴansandan Jihar Delta, DSP Bright Edafe ya tabbatarwa da faruwar lamarin a tattaunawarsa da DAILY POST ta wayar salula, sai dai ba shi da cikakkiyar masaniya kan mutuwar ƴansandan.
