For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ɓaraka A APC Yayin Da Abdullahi Adamu Ke Fuskantar Barazana Kan Salon Shugabanci

An samu ɓaraka a Kwamitin Shugabancin Jam’iyyar APC na Ƙasa saboda kasancewar wasu mambobin ba sa tare da Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu.

Wannan ɓaraka ta baiyana ne yayin da jam’iyyar APC ke shirye-shiryen fara babban taronta na ƙasa domin zaɓar ɗan takarar Shugaban Ƙasa wanda zata yi a ranakun 6, 7 da 8 ga watan Yuni mai kamawa.

Ɓarakar da ke cikin Kwamitin Shugabancin Jam’iyyar an alaƙanta ta ne da salon mulkin Abdullahi Adamu da ke fuskantar zazzafan kushe.

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na yankin Arewa maso Yamma, Salihu Mohammed Lukman ya turawa Abdullahi Adamu wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 27 ga watan Mayu, 2022 da kuma take: “Sake Gina APC: Buƙatar Samun Sabbin Tsare-tsare”, inda a cikinta ya nuna buƙatar kaucewa kurakuren da shugabannin jam’iyyar na baya suka yi.

Ya yi zargin cewa, sabon zubin shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu, na juyewa a hankali yana komawa irin na Adams Oshiomole da Mai Mala Buni inda ake yanke hukunci ba tare da an zartar ba, sannan kuma ba a tafiya da sauran mambobi wajen tsara al’amura.

A wasiƙar an rubuta cewa, “A ƙarƙashin shugabancinka, Kwamitin Shugabancin Jam’iyya na Ƙasa na juyewa zuwa makamancin yanayi irin wanda ake yanke hukunci a ƙyale babu zartarwa ko kuma a wani lokacin a canja hukunci ba tare da an tuntubi sauran mambobi ba.

“Har yanzu ba a tantance masu neman takarar shugabancin ƙasa ba. Bayanin ba ya wuce kana jiran ganawar ƙarshe da Shugaban Ƙasa Buhari ba. Duk na san za a ga na matsa, amma wannan rashin adalci ne ga Shugaban Ƙasa, saboda a fahimtata, ana so a yi fake da shi ne domin samun mafita idan an samu matsala.

“Na ga cewa, ya zama dole na turo maka wannan takarda domin na roƙe ka da ka gyara yanayin yanda muke abubuwanmu a Kwamitin Shugabancin Jam’iyya na Ƙasa ƙarƙashin kulawarka. Yanzu haka watanninmu biyu da fara shugabanci, kuma ka sanya cewa za a samu gyara kan matsalolin da suka daƙushe samun goyon baya ga shugabancin da ya gabata.

“Alal misali, yanzu haka ana zaman Kwamitin Shugabancin Jam’iyya na Ƙasa duk sati. Mambobi suna bayar da gudunmawa yanda ya kamata kuma suna shiga da aiwatar da abubuwa.

“Abun a yaba maka ne cewa, kana yarda da matsayar mambobi ko da kuwa ta saɓa taka. Wannan wani ci gaba ne kan tsarin shugabancin baya inda Shugaban Jam’iyya ke gudanar da zaman tarurrukan jam’iyya a matsayin mai ba da umarni, hakan kuma ya ke jawo danniya ga mambobi.

“Babban ƙalubale shine tabbatar da cewa an aiwatar da matsayar da aka amincewa yanda ya kamata. Gazawar shugabancin da ya gabata ƙarƙashin Adams Oshiomole da Mai Mala Buni wajen aiwatar da matsayar da aka cimma ita ce, ta jawo rikicin shugabancin da a wancan lokacin ya addabi jam’iyyar.

Salihu Muhammed Lukman ya tura kofin wasiƙar tasa ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari; Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo; Shugaban Majalissar Dattawa, Ahmed Lawan; Kakakin Majalissar Wakilai, Femi Gbajabiamila; Cif Bisi Akande; Asiwaju Bola Ahmed Tinubu; Kwamared Adams Oshiomole; Chief Ogbonayan Onu da kuma duk sauran mambobin Kwamitin Shugabancin Jam’iyya na Ƙasa.

Comments
Loading...