For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ɗan Majalissar Jiha Ya Samar Da Wutar Sola A Babban  Masallacin Birnin Kudu

Ɗan Majalissar Jiha mai wakiltar, Mazaɓar Birnin Kudu a Majalissar Jihar Jigawa, Muhammad Kabir Ibrahim ya samar da hasken wutar lantarki a Babban Masallacin Birnin Kudu.

Ɗan Majalissar ya samar da wutar ne ta hanyar sanya kayan samar da wuta ta hanyar hasken rana, inda aka samar da wutar da zata haskaka makeken masallacin gabaɗayansa da kuma bayar da wuta ga kayan magana da kuma fankokin masallacin.

Babban masallacin Birnin Kudu dai ya jima yana fama da matsalar hasken wutar lantarki, abin da ke sanya rashin samun cikakkiyar nutsuwa ga masallata da sauran masu ibada a masallacin, musamman a lokacin zafi.

Maigirma Sarkin Kudu, Alhaji Garba Hassan Jibrin, shine jagoran kwamitin da ke kula da masallacin, ya nuna jin daɗinsa da farincikinsa kan ƙoƙarin ɗan majalissar, inda ya ce ɗan majalissar ya biya musu buƙatar da suka jima suna son su ga an biya musu.

Ya yi kira ga sauran wakilan al’umma da su yi koyi da irin wannan aikin alkhairi, musamman ma ganin cewar shi ɗan majalissar da kansa ya gano buƙatar masallacin ya yi aikin ba tare da an tuntuɓe shi ba.

Ɗan Majalissa, Muhammad Kabir Ibrahim ya bayyanawa TASKAR YANCI cewar, a shirye yake wajen sauƙe nauyin da al’ummar mazaɓar Birnin Kudu suka ɗora masa, sannan kuma zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ya inganta rayuwarsu.

Comments
Loading...