Karamin Ministan Ƙwadago da Samar da Aikin Yi, Festus Keyamo ya bayyana cewa, irin tsarin da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bi wajen shugabancin Najeriya irinsa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu zai bi wajen shugabancin Najeriya idan ya samu lashe zaɓe.
A ranar Juma’ar da ta gabata, ministan ya ce kasancewarsa mai alfahari da irin jagorancin APC a ƙasar nan, dukkan shugabannin biyu (Buhari da Tinubu) suna kan tsarin APC iri ɗaya ne.
Na kusa da Tinubu kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Adams Oshiomhole, a daren Alhamis ɗin da ta gabata ya buƙaci da a cire Tinubu daga gazawar gwamnatin Buhari, inda yai iƙirarin cewa tsohon gwamnan Jihar Legos bai kasance cikin gwamnatin Buharin ba.
To amma Keyamo wanda minista ne mai ci a yanzu, ya faɗa a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels cewa, ƴan jarida ne suka juya maganar ta Oshiomhole.
“Tsarin APC ne guda ɗaya da su shugabannin biyu (Buhari da Tinubu) zasu yi amfani da shi. Na ga wani taken labarai na ƙarya a ɗa wata daga wata jarida daga jaridu a jiya kuma sai nai dariya. Ba gaskiya ba ne, juya abun da shugabanninmu suka faɗa. Cewa muna nesanta kanmu daga abubuwan da Buhari ya yi; wannan rashin hankali ne. Kamar yanda na faɗa, muna alfahari da abubuwan da APC ta yi,” in ji Keyamo.
Ministan ya jaddada cewa Tinubu yana alfahari da abubuwan da gwamnatin Buhari ta yi.
Ya ce ta yiwu Tinubu ya canja wasu daga tsare-tsaren gwamnati “a kan tsarin samar da ci gaba (irin na APC)”.
Najeriya ta samu tasgaro a ɓangarorin ci gaban ƙasa da dama cikin shekaru 7 na Shugaba Buhari tare da samun ƙaruwar matsalolin tsaro da kuma lalacewar tattalin arziki.
Jami’o’in gwamnati suna kulle kusan watanni shida yayin da malaman jami’o’in ke ci gaba da kukan rashin kyawun yanayin aiki.
A shekarar 2018, Najeriya ta doke Indiya inda ta zama cibiyar talauci ta duniya, kamar yanda rahoton Brookings Institution ya bayyana, yayin da kuma bashin da ake bin Najeriya ya kai naira tiriliyan 41.60 a karkashin kulawar gwamnatin Buhari kamar yanda Ofishin Kula da Basussuka ya bayyana.
A baya dai SAHARAREPORTERS ta rawaito cewa, a lokacin da yake jawabi kan matsalar tsaro a lokacin gwamnatin Buhari, Keyamo ya ce, a lahira ne kaɗai ba za a sami matsalar tsaro ba.
“Matsalar tsaro ce, zata ƙara faruwa a gaba? Gwamnati zata mayar da martani yanda ya kamata? Zasu yi. Abin kaico, akwai matsalar tsaro a ko’ina a duniya, amma ba wannan ne abun dubawa ba a ce gwamnati ta gaza. Ana ɓalle gidajen yari. A ƙasashen Turawa: ana ɓalle gidajen yari. Ba wai ina alfahari da hakan ba ne,” in ji shi.