Tshohon Gwamnan Jihar Anambra kuma tsohon ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa a PDP a shekarar 2019, sannan ɗaya daga cikin masu neman Jam’iyyar PDP ta amince musu domin yi mata takarar Shugaban Ƙasa a 2023, Peter Obi, ya ajjiye takararsa tare da ficewa daga Jam’iyyar PDP.
Wannan na zuwa ne kwanaki biyu kacal kafin Jam’iyyar PDP ta fara zaɓen fidda gwanin da zai mata takarar Shugaban Ƙasa a shekarar 2023n.
Peter Obi ya baiyana cewa, suna kan tattaunawa da jam’iyyun Labour Party, SDP da ma wasu jam’iyyun kuma zai sanar da sabuwar jam’iyyar da zai shiga cikin awanni 24 masu zuwa.
An gano cewa Peter Obi na ƙoƙarin haɗewa da haɗakar jam’iyyu wanda ke nufin kawar da jam’iyyar APC mai mulki da kuma jam’iyyar PDP da nufin ceton Najeriya, bayan ya gaza shawo kan masu zaɓen ƴan takara a PDP kan ƙudirinsa.
A wasiƙar barin takara a PDP wadda ya turawa Shugaban Jam’iyyar, Iyorchia Ayu, Peter Obi ya ce, ya ji daɗin bayar da gudunmawar da yai wajen gina PDP.
Ya ƙara da cewa, abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar PDP a halin yanzu, ba zasu bar shi ya ci gaba da kasancewa a jam’iyyar ba, saboda haka, ya janye neman takarar Shugaban Ƙasa da yake yi a jam’iyyar.
Peter Obi ya kuma sanar da cewa, ya tura takardar ficewa daga PDP ga shugaban jam’iyyar na mazaɓarsa ta Agulu ta 2 da ke Ƙaramar Hukumar Anoacha a Jihar Anambra, kuma fitar tasa daga jam’iyyar ta fara aiki tun ranar Juma’a, 20 ga watan Mayu, 2022.