For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Majalissar Dinkin Duniya Ta Ce Dole A Kawo Karshen Muzgunawa ‘Yan Jarida

Daga: BBC Hausa

Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don tunatarwa game da kokarin kawo karshen aikata muggan laifuka da suka danganci cin zarafin ‘yan jarida.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteress ya yi kira ga kasashen duniya da su tashi tsaye wajen nuna goyon bayansu ga ‘yan jarida da sauran ma’aikatan kafafan yada labarai a fadin duniya.

Mr Gutteres ya kuma bukace su da su yi iya yinsu wajen bincika tare da hukunta duk wanda ya aikata cin zarafi da gallaza wa manema labaran.

A kasashe da dama manema labarai na fuskantar matsaloli yayin gudanar da ayyukansu, da suka hada da cin zarafi da gallazawa, da hana ‘yancin samun bayanai da na fadin albarkacin baki da ma samar da bayanan ga jama’a.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniyar ya ce ‘yan jarida ko kuma manema labarai kimanin 1,200 a fadin duniya aka hallaka a tsakanin shekarar 2006 and 2020 yayin da suke gudanar da aikinsu.

Rahoton ya kuma ce duk da haka ba a hukunta wadanda suka aikata kisan ba.

Kasashen da aka fi kashe ‘yan jarida a duniya sun hada da Syria da Philippines da Iraki da kuma Pakistan.

Sauran sun hada da Somaliya da Indiya da Mexico da Rasha da Sri Lanka da kuma Brazil.

Majalisar Dinkin Duniya ta kuma bayyana cewa kashi 73 cikin dari na mata ‘yan jarida na fuskantar barazana da cin zarafi ta kafafen sada zumunta don kawai sun gudanar da aikinsu.

Comments
Loading...