Bayan nazari da bincike tareda bibiyar matasa da kuma ƙungiyoyi, mu matasa munyi ittifakin cewa MAGAJIN BABA shine ya fi cancanta da al’ummar Birnin Kudu/Buji mu miƙawa amanar jagorantar yankin a Majalissar Wakilai ta Tarayya a shekarar 2023 mai zuwa.
Mu dandazon matasa ne masu son cigaban Birnin Kudu/Buji, karkashin ƙungiyoyin mu matasa masu manufa iri daya, ta samar da nagartaccen jagoranci a Birnin Kudu/Buji a shekarar 2023.
Burin matasa shine, tabbatar cigaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma gaba ɗaya.
Mun amince cewar, ci gaban al’ummarmu yana cikin tsaiko a zaune, burin namu shine samarwa matasa madogara da kuma aiyukan yi, abin da mu matasa muka amince cewa MAGAJIN BABA shine mafi cancanta domin tabbatar da hakan a Birnin Kudu/Buji.
Muna da yakinin cewa idan MAGAJIN BABA ya samu nasarar zama Dan Majalissa mai Wakiltar Birnin Kudu/Buji a Majalissar Tarayya, za a samu cigaba a fannonin harkar lafiya, cigaban tattalin arziki, da kare muhalli, samun shigowar masu sanya hannun jari da dai sauran alherai.
Haka kuma mu matasa muna da hasashen Birnin Kudu/Buji zamu samu bunkasar harkar cigaban sadarwar zamani, fasaha da kere-kere da kuma gagarumin cigaba a fannin noma da kiwo.
MAGAJIN BABA mutum ne mai nagarta tareda biyayya ga tsarin demokaraɗiyya wadda ke baiwa kowa dama iri daya wajen bayar da gudummawa domin bunkasa al’umma baki daya.
Bayan haka MAGAJIN BABA matashi ne, kuma a duk inda matasa suke a nan ake samun canji, duk inda matasa suke anan ƙashin bayan al’umma yake, duk inda matasa suke sun fi kowa yawa a ko inane, a duk inda matasa suke matashi dan’uwansu shine yasan matsalarsu har ya kawo musu mafita.
RA’AYI: Umar Ɗahiru Musa