Biyo bayan nasarar da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya samu a zaɓen fidda gwani na takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar PDP a ranar Asabar da ta gabata, an shigar da sabuwar ƙara a kan sa, a Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, ana buƙatar a hana shi tsayawa takarar a zaɓen Shugaban Ƙasa mai zuwa.
TASKAR YANCI ta rawaito cewa, Atiku Abubakar ya lashe zaɓen fidda gwani na takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar PDP, bayan ya samu ƙuri’u 371 inda ya doke Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike da tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Bukulo Saraki da sauran ƴan takara.
Ƙarar da aka shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/751/2022, wani lauya ne mazaunin Abuja mai suna, Johnmary Jideobi ya shigar a jiya Talata, yana ƙalubalantar cancantar Atiku bisa la’akari da kundin tsarin mulkin Najeriya wajen tsayawa takarar Shugaban Ƙasa.
Ya buƙaci kotun da ta warware matsaloli bakwai a kan Atiku, PDP da kuma Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta, INEC, waɗanda aka ambata a matsayin waɗanda ake ƙara na ɗaya, na biyu da kuma na uku, haka kuma an shigar Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya a matsayin na huɗu a waɗanda ake ƙara.
Mai ƙarar ya buƙaci kotun da ta warware ma’anar “Ko, haɗakar tanade-tanade a sassa na 1(1) da (2), 25 da 131(a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na Shekarar 1999 (wanda aka yi wa gyara) sun biyana cewa iya wanda aka haifa a Najeriya ne kaɗai zai iya zama Shugaban Ƙasa a Najeriya?
“Ko haɗakar bayanan sassa na 1(1) da (2), 25(1) da (2) da kuma 131(a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na Shekarar 1999 (wanda aka yi wa gyara) da kuma abubuwan da suka zagaye batun haihuwar wanda ake ƙara na ɗaya (wato Atiku Abubakar) zai iya samun dama daga wanda ake ƙara na biyu (wato PDP) da wanda ake ƙara na uku (wato INEC) ta tsayawa takarar Shugaban Ƙasar Najeriya?”
Ya kuma ce, dole ne kotu ta tabbatar da cewa, INEC ba ta bar duk wani mutum ko wasu mutane sun jagoranci gwamnatin Najeriya ba ko wani ɓangare na gwamnatin har sai an bi tanade-tanaden kundin tsarin mulki.
Daɗindaɗawa, Lauya Jideobi ya yi fatan cewa, kotu zata aiyana, “duba da sassa na 1(1) da (2), 25 da kuma 131(a) na Kundin Tsarin Mulki cewa, iya wanda ya zama ɗan Najeriya ta hanyar haihuwa ne kaɗai wanda Kundin Tsarin Mulki ya amincewa ya tsaya takarar shugabancin ƙasa a Najeriya.
Ya ƙara da buƙatar a aiyana cewa, “duba da yanayin yanda haihuwar wanda ake ƙara na farko (wato Atiku) ta kasance, bai cancanci a dokokin kundin tsarin mulki a bar shi ya tsaya neman takarar Shugaban Ƙasar Najeriya ba.”
Wanda ke ƙarar na buƙatar “kotu ta bayar da umarnin hana wanda ake ƙara na farko (wato Atiku Abubakar) tsayawa takarar neman shugabancin Najeriya.”
Ya kuma buƙaci kotu ta aiyana cewa “Jam’iyyar PDP ba ta da ɗan takarar Shugaban Ƙasa a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, wanda (INEC) da ake ƙara a matsayin ta uku take shiryawa.”