For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

2023: Atiku Zai Yi Zango Daya Ne Ya Sauka Idan An Zabeshi Shugaban Kasa – Dokpesi

Shugaban bangaren tsare-tsare na yakin neman zaben Atiku Abubakar a matsayin dan-takarar shugaban kasa, Raymond Dokpesi ya ce, idan har an zabi tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasa, zai yi mulki na wa’adi daya ne kacal.

Dokpesi, wanda yai jawabi a garin Umuahia na jihar Abia a jiya Litinin, ya tabbatar da cewa, Atiku Abubakar wanda ya fito daga yankin Arewa maso Gabas shine wanda ya fi cancanta ya kwaci mulki daga jam’iyyar APC.

Ya bayyana cewa, alamu na nuna cewa, dalilin Atiku yankin Kudu maso Gabas zai samu damar fitar da shugaban kasa a shekarar 2027.

KU KARANTA: Gwamnonin PDP Sun Zargi Jam’iyyar APC Da Ruguza Tattalin Arzikin Najeriya

Da yake bayyana wasu daga cikin dalilan da suka jawo tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya fadi zaben 2015, Dokpesi ya ce, rashin mutunta tsarin karba-karba ne ya jawo matsalar faduwa zaben.

Ya ce, a dalilin haka, jam’iyyar ta shiga zaben da rarrabuwar kai wadda sanadiyyar faduwarta.

Dokpesi ya ce, ya kamata jam’iyyar PDP ta baiwa yankin Arewa dama domin kammala karashen shekaru hudunta a shugaban kasa a matsayin hanyar kwace mulki daga APC a 2023.

Ya ce, “Jam’iyyarmu ta yarda da tsarin karba-karba tsakanin Kudu da Arewa na tsawon zango biyu wato shekaru takwas. Wanna ta sa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya mika mulki ga Marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua, amma bayan mutuwarsa, tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya karbi mulki ya karasa zangon farko.

“Bayan haka, Jonathan ya nemi a kara masa wasu shekaru hudun, kuma aka kara masa, amma lokacin da ya fara neman karin wasu shekaru hudun a 2015, Arewa ta ji cewar tsarin ya sabawa yarjejjeniyar jam’iyyar ta karba-karba.

“Saboda haka muka shiga zabe da rarraben gida kuma muka fadi zabe. Wannan ta sa mukai tunani cewa, domin mu kwaci mulki daga APC, akwai bukatar kwakkwaran dan-takara daga yankin Arewa.

“Tun da an tabbatar da cewa, yankin Arewa maso Gabas da Kudu maso Gabas ne yankunan da ba su fitar da shugaban kasa ba, mun yarda cewa Atiku, a matsayinsa na dan yankin Arewa masu Gabas, shine mafi cancanta da mukamin.”

Shugaban PDP na jihar Abia, Alwell Asiforo, ya tabbatarwa masu ziyarar cewa, jam’iyyar a bude take ga kowa da yake da kudirin takara wanda ya ziyarci jihar domin tuntuba.

Comments
Loading...