For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

2023: Indai Cancanta Ake Magana, Pharm. Hashim Ubale Ya Fi Sauran ‘Yan Takarar A Jigawa

Matukar chanchanta ake nema wajen shugabanci, al’ummar Jigawa zasu baiwa Pharm. Hashim Ubale Yusufu ragamar darewa kan kujerar gwamnan jihar Jigawa a shekarar 2023.

Sanin kowanne dan Jigawa ne Pharm Hashim Ubale Yusufu tsohon ma’aikacin gwamnati ne kuma tsohon gogaggen dan siyasa da ya rike manya manyan mukamai a matakin jihar Jigawa, tarayya har ma da wasu hukumomin kasa da kasa da hakan zai matukar yin tasiri wajen tafiyar da jihar da kuma dorata a kan tsari na cigaba, ba tare da nuna bangaranci ko bambancin siyasa ba.

Idan mukai duba ga mukamin kwamishina daya rike lokacin gwamnatin Alh. Ibrahim Saminu Turaki, kai tsaye muna iya cewa kaso mafi tsoka na nasarorin da gwamnatin ta samu sun samu ne da gudummawar Pharm. Hashim Ubale, domin ga misali ayyukan lantarki da gwamnatin lokacin ta gudanar, Pharm. ne ya jagoranci aiwatarwa wadda har aka kai ga kafa babbar tashar lantarki a Gagarawa da manufar samar da lantarki mallakar jihar Jigawa.

A zagayen samar da wuraren da za’a sada da lantarkin ne kuma ya gano wasu muhimman hanyoyi da ya kamata a samar a jihar, saboda rashinsu ya haifar da tsananin wahala ga mazauna yankunan da abin ya shafa, ya rubuta a cikin rahotonsa domin a samar da su, gwamnatin wancan lokacin da sauran gwamnatoci biyun da suka biyo baya kusan duk da wancan rahoton da ya bayar sukai amfani wajen gina hanyoyin da a yanzu ake alfahari da su a Jigawa.

Pharm. Hashim Ubale Yusuf ne mutum na farko a tarihin jihar Jigawa da ya shirya tare da kaddamar da taron masu kananan sana’o’i da masana’antu a Jigawa domin ingantawa da habaka harkokin kasuwanci da tattalin arziki a jihar, wanda ba a kara yin makamancin taron ba sai a gwamnatin data gabata da suka kira taron da suka kira da ‘Talakawa Summit’.

Akwai manyan ayyuka da dama da ba zasu fadu a takaitaccen rubutu irin wannan ba. Amma idan muka kalli ko da a jam’iyyar APC shine ya fara samawa jam’iyyar ofishin gudanar da ayyukanta na farko.

Kazalika shine ya sayawa daukacin shuwagabannin jam’iyyar APC da sukai takara a mukaman shugabancin jam’iyyar daban-daban tun daga mazabu har jiha a wancan lokacin, wanda har yanzu babu wanda ya taba ko da kwatanta hakan, bugu da kari kuma har yanzu duk da rashin nasarar samun tikitin yiwa jam’iyyar takara har karo biyu, shine mutum daya tilo da yake cigaba da baiwa Gwamna Muhammad Badaru Abubakar gudummawa domin ciyar da jihar Jigawa gaba wanda hakan shine fatansa a kullum.

Don haka, matukar cigaba ake bukata bisa chanchanta, ‘yan Jigawa ba zasu taba mantawa da gudummawar da Pharm. Hashim Ubale Yusufu ya bayar wajen cigaban jihar ba, kuma zasu mara masa baya wajen dora jihar bisa tafarkin cigaba mai dorewa a 2023.

Rigar ‘Yanci – Ra’ayi: M A Birnin Kudu

Comments
Loading...