For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

2023: Kiraye-Kiraye Sun Kai Makura A Kan Mustapha Sule Lamido – Baffa Danhaya

Babban zaben shekarar 2023 yana kara kusantowa, a yayinda kiraye-kiraye sukai yawa a Nijeriya kan matasa domin su karbi jagorancin shugabanci a dukkannin matakai na kasar, kamar dai yadda kasashen duniya wadanda suka ci gaba suke a halin yanzu.

A Jihar Jigawa ma ba a barmu a baya ba, sakamakon yadda kungiyoyi da jama’ar jihar suke ta kiraye-kiraye a kan Alhaji Mustapha Sule Lamido da ya fito takarar Gwamnan Jihar a karkashin tutar jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2023.

Ko shakka babu, Alhaji Muatapha Sule Lamido wanda shi ne Santurakin Dutse wanda kuma matasan Jihar Jigawa ke masa lakabi da GOBE TA ALLAH CE yana daya daga cikin masu ruwa da tsaki da za a dama dasu a zaben 2023 domin mutum ne jajirtacce, masanin ilimin Kimiyar Siyasa (Political Science), dan-kasuwa kuma dan-siyasa wanda ya yi takarar Majalisar Dattawa a shekarar 2019 yana neman wakiltar Mazabar Jigawa ta Tsakiya.

Hakan tasa kungiyoyi da al’umma da dama ke ta kira a gareshi domin ya fito takarar Gwamnan Jihar a zabe mai zuwa na shekarar 2023.

Irin wadannan kungiyoyi sun hada da: Kungiyar Matasan Cigaban Jihar Jigawa, Kungiyar Kwararrun ‘Yankasuwa, Kungiyar Matasa Masu Kishin Jihar Jigawa, Kungiyar Jigawa Kawai da dai sauran kungiyoyi daban-daban wadanda jihar ce a gabansu, suna ta matsa lamba a kan ya amsa kiransu domin a ceto jihar daga halin da take ciki a yanzu.

Da yawa daga cikin al’ummar Jigawa sun yi imanin cewa idan Allah ya bawa Alhaji Mustapha Sule Lamido jagorancin jihar a zabe mai zuwa, tabbas za’a samu cigaba kamar yadda mahaifinsa ya gina jihar domin sai Jigawa ta yi gogayya da sauran jahohin Nigeria.

Saboda haka ne, muke kira tare da rokonsa da ya amsa kiran al’umma, ya fito takarar Gwamnan Jihar Jigawa a 2023.

Comments
Loading...