For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

2023 : Wike Na Faɗa Da Yankin Arewa Ne – In Ji Wata Kungiyar Matasa

Shugaban ƙungiyar wayan dakan yan arewacin Najeriya (NAM) , Muhammad Inuwa, ya bayyana wannan kalaman cin mutuncin da gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike yake akan Atiku Abubakar da wani salone na cin mutuncin arewacin ƙasar nan.

Inuwa yayin da yake tofa albarkacin bakinsa akan kalaman na Wike, ya ce lokaci ya yi da ya kamata a kira Wike a dawo dashi cikin hayyancinsa tun kafin ya jefa ƙasar cikin matsala.

Wannan rikicin da Wike yake dashi da jama’arsa ya samu asalin tun daga kayen da ya sha a zaɓen cikin gida da PDP ta yi domin fitar da wanda zai mata takarar shugaban ƙasa.

Muhammad Inuwa, yayin da yake tattaunawa da yan jarida a babban birnin jihar Kebbi , ya ce bayan da aka yi dukkan mai iyuwa wajen shawo kan Wike amma yaki yarda to tabbas akwai wata ƙullalliya a ƙasa.

“Mun samu wani labarin sirri dake nuna mana dukkan waɗannan abubuwan da yake yana yi ne da manufar kada arewacin ƙasar nan suyi nasara a babban zaɓen dake tafe.

“Muna da cikakkiyar sheda da ta nuna mana dukkan wannan abun da Wike yake da mutanensa suna yi ne domin cin zarafin arewacin ƙasar nan.

“Daga ƙarshe mun gano cewa Wike da dukkan yan tawagarsa sun kulla yaki ne da arewacin Najeriya. Wannan ƙungiyar da take kokarin wayar da kan mutanen arewa tana kira ga dukkan wani mai faɗa a ji da su ja hankalin Wike a kan wannan abun da yakewa arewa” in ji Muhammad Inuwa.

Daga ƙarshe muna sanar da cewa, dukkan ƙungiyoyin arewa ba zasu zuba ido Wike da yan tawagarsa suna cin mutuncin arewa ba. Kuma zamu dau dukkan matakin da ya dace idan bai shiga taitayinsa ba .

Comments
Loading...