For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

2023: Ƴan Gani Kashenin Kwankwaso Sun Yi Mubaya’a Ga Sule Lamido

Waɗansu ƴan gani kashenin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso sun nuna mubaya’arsu ga tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido.

Tun dai lokacin da Kwankwaso ya yanke hukuncin barin jam’iyyar PDP domin ya koma jam’iyyar NNPP ake samun ɓaraka a sananniyar tafiyar siyasar nan ta Kwankwasiya, inda ake samun jiga-jigan tafiyar suna nuna bijirewa ga tsohon jagoran nasu wajen shiga NNPP.

Wata majiya a wajen zaman wanda aka gudanar a gidan Sule Lamido da ke Kano ta ce, cikin magoya bayan tsohon Gwamna Kwankwason da suka halarci zaman akwai tsofin Kwamishinonin Kwankwaso a lokacin da yai mulki a 2011 zuwa 2015.

Irin waɗannan mutane sun haɗa da Dr Yunusa Adamu Dangwani, Yusuf Bello Dambatta da Farfesan Ilimin Harkokin Yada Labarai, Dr. Umar Faruk Jibril, da kuma Abubakar Nuhu Ɗanburan.

A lokacin zaman, tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido ne ya jagoranci zaman a matsayinsa na dattijo kuma jagoran jam’iyyar PDP a Najeriya.

An rawaito cewa Sanata Bello Hayatu Gwarzo ma yana wajen zaman na masu ruwa da tsaki na PDPn Kanon.

Bayan kammala zaman, masu ruwa da tsakin sun yi kira ga Shugabancin Jam’iyyar PDP na Ƙasa da su rushe jagorancin jam’iyyar a Jihar Kano tare da naɗa shugabannin riƙon ƙwarya nan take.

Ɗaya daga cikin dalilan da suka baiyana shine cewa, tsohon Gwamna Kwankwaso yana yin maƙarƙashiya ga jam’iyyar PDP a Kano, inda a lokaci guda yake gina sabuwar jam’iyyarsa ta NNPP.

Sun baiyana cewa, idan har ba a gaggauta daukar mataki ba, ƙoƙarin Kwankwaso shine ya hana jam’iyyar PDP tsayar da kowanne ɗan takara a zaɓen 2023, saboda haka ne Shugabancin Jam’iyyar a jihar, ya ƙyale magoya bayan jam’iyyar cikin rashin sanin makama.

Sun ce, lokaci na ƙarshe na siyar da fom ɗin tsayawa takara a PDP shine 1 ga watan Afrilu, 2022, hakan zai hana jam’iyyar PDP damar fitar da ƴan takarkaru ya baiwa jam’iyyar NNPP dama da sauran jam’iyyu.

(NIGERIAN TRACKER)

Comments
Loading...