For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

A Binciki Tsoffin Shugabanni, A Sake Sunan Najeriya, In Ji Wani Babban Lauya

Babban Lauyan Najeriya, SAN, kuma tsohon Shugaban Ƙungiyar Nigerian Body of Benchers, Chief Wole Olanipekun, ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya binciki tsoffin shugabannin Najeriya domin gano yanda akai ƙasar ta dagule haka.

A cewarsa, tsoffin shugabanni suna tambayoyin da za su amsa game da ƙarancin ababen more rayuwa, tagayyararren tattalin arziƙi da kuma matsalar tsaro da addabi ɓangarori da dama na ƙasa da ma sauran tambayoyi.

Olanipekun, wanda yai magana a wajen wata liyafa a Abuja domin murnar cikar Joe-Kyari Gadzama shekaru 25 da zama SAN, ya ce, maƙudan kuɗaɗen da aka warewa ɓangarorin ci gaban tattalin arziƙi da dama dole ne a bincike su.

KARANTA WANNAN: PDP Ta Cika Shekaru 25 Da Kafuwa, Ta Ce Shekarunta Na Mulki Ne Gwalagwalai Ga Najeriya

Ya ƙara da cewar, dole ne gwamnati ta binciki dalilin da ya sa darajar naira tai matuƙar faɗuwa wanwar har ta zabgo ƙasa zuwa naira 900 a dalar Amurka 1.

Ya kuma yi kira da a sake sunan Najeriya, inda ya ce, sunan da ake amfani da shi yanzu ƙasƙanci ne da kuma munafurci, saboda haka ya kamata ƴan Najeriya su dena zagin kansu da ci gaba da zama da sunan da matar Lugard ta ba su.

Ya ce, abin takaici ne  a ce har kawo yanzu, ƴan Najeriya ba su samu ƙarfin guiwar ajjiye sunan ba, inda ya ƙara da cewar, ƴan Faransa sun sa wa waɗanda su ka yi wa mulkin mallaka Nijar yayin da ƴan Birtaniya suka sanya mana Najeriya.

Ya yi tambayar cewar, mene ne banbancin sunan Nijar da Najeriya in banda Faransanci da Turanci?

Comments
Loading...