For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

A Karon Farko Sule Tankarkar Ta Raba JAMB 60 Ga Dalibanta

Shugaban Karamar Hukumar Sule Tankarkar da ke Jihar Jigawa, Saleh Ahmad Danzomo, ya raba lambobin yin rijistar Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB ga wasu dalibai ‘yan asalin karamar hukumar da yawansu ya kai 60.

An zakulo daliban ne daga ɓangarori daban-daban na karamar hukumar, wadanda suka hada da ‘ya’yan marassa karfi da kuma marayu mata da maza.

Shugaban karamar hukumar ya damka wadannan lambobi na JAMB ga Kungiyar Dalibai Y’an Asalin Karamar Hukumar Sule Tankakar, SULSA domin ta raba ga daliban da aka zakulo.

Ya kuma gargadi shuwagabannin kungiyar a kan cewa su cire son zuciya su wajen rabon, su tabbatar sun raba ga rukunin daliban da suka fada wadanda aka tanada domin su.

Wannan dai shine karo na farko a tarihin karamar hukumar, da wata gwamnati ta karamar hukuma ta taba bayar da  irin wannan tallafin.

A ranar Asabar da ta gabata ne dai, 19 ga watan Fabrairu na 2022 JAMB ta fara rijistar masu sha’awar rubuta jarabawar a bana.

Comments
Loading...