Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa a mulkinsa wajen kin zuwa waje neman magani idan aka zabe shi shugaban kasa a shekarar 2023.
Ya yi wannan alkawarin ne lokacin da yake magana a Taron Al’umma 2023 wanda Channels Television ta gabatar a daren jiya Lahadi.
Lokacin da aka tambaye shi kan shirye-shiryensa a bangaren lafiya idan ya zama shugaban kasa, Kwankwaso ya ce, “Zan yi duk iya kokari na, ba zan je ko ina (waje) domin neman magani ba.
“Matsalar da muke da ita a yau, wanda muka ce zamu gyara, ya shafi kowanne bangare, har da bangaren lafiya kuma ina farincikin sanar da ku cewa shirinmu zai fara ne da fannin ilimi kamar yanda muka yi a Kano. Mun gina makarantu biyar a karkashin ma’aikatar ilimi – makarantun koyon aikin jinya guda biyu, makarantun ungozoma guda biyu da kuma kwalejin koyon fasahar lafiya guda daya.
“Mun tura maza da mata kasashen waje kari a kan tallafin karatun da muka bayar don a koyo aikin likitanci. Mun ciyar da dukkan asibitocinmu gaba.
“Mun baiwa asibitocin muhimmanci, ganin irin kayayyakin da suke cikin [asibitocin kasashen waje] kuma fa babu wanda Najeriya ba zata iya siya ba. Saboda haka babu wani gagarumin banbanci da abun da muke da shi a asibitocinmu.”
Tsohon Gwamnan na Jihar Kano ya ce, gwamnatinsa zata shigo da ma’aikata su kula da kayan aiki a asibitocin Najeriya kamar dai yanda ‘yan Najeriya ke fita kasashen waje don su yi aiki.
Ya yi alkawarin kawar da duk wani kalubale da ke hana ma’aikatan lafiya samun ci gaba, inda ya tuna cewa, a matsayin gwamnan Kano, daya daga cikin zakakuran daliban likitanci daga wata jami’a ta kasa samun damar karbar horo har sai da ta zo ta same shi don ya temaka mata.
“Sai ka san wani kafin ka samu horo (housemanship), amma zamu kawar da duk irin wadannan kalubalen.”
Tsohon gwamnan Kanon ya ce, bangaren ilimi shine zai zama kan gaba a gwamnatinsa, inda ya kara da cewa za a sanya karin kudade a matakan ilimi daban-daban.
Da yake korafi kan yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasa, ya ce jadawalin kudire-kudirensa zai hana yara gararanba a kan tituna zai kuma gina karin makarantu a kasa.
Kwankwaso ya kuma yi alkawarin magance dadaddiyar matsalar cin hanci da rashawa ya kuma karawa bangaren makamashi karfi domin farfado da masana’antu a bangaren tattalin arziki.
Ya kuma kawar da zargin cewa shi ya tsufa wajen fuskantar tarun matsalolin da ke fuskantar kasa, inda ya ce ya ma fi sauran ‘yan takarkarun cikar lafiya da karfin jiki.