Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa yana shirye ya ɗauki tsauraran matakai don ciyar da ƙasa gaba, duk da cewa ba koyaushe ake samun haɗin kan ƴan ƙasa kan batutuwan ba.
Tinubu ya yi wannan bayani ne a Beijing lokacin da yake ganawa da ƴan Najeriya mazauna ƙasar Sin, inda ya bayyana ziyararsa a matsayin mai ma’ana kuma mai nasara.
Ya jaddada cewa ya mayar da hankali wajen ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da China a fannonin ababen more rayuwa, kasuwanci, kuɗi, makamashi, tattalin arzikin noma, da hakar ma’adinai.
Tinubu ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da ke zaune a China da su ci gaba da wakiltar ƙasar a matsayin nagartattun mutane yana mai jaddada mahimmancin tarbiyya da halayya ta gari wajen gina ƙasa mai ɗorewa.
Ya bayyana cewa koyo daga tsarin rayuwa mai tsauri na ƙasar Sin na da matuƙar muhimmanci, inda ya jaddada cewa dole ne a nuna ƙwarewa da biyayya ga doka don ciyar da Najeriya gaba.
Tinubu ya tabbatar wa ƴan Najeriya mazauna ƙasar Sin cewa Bankin Masana’antu na Najeriya zai taimaka musu wajen amfana da damar zuba jari a gida, tare da tabbatar da cewa ya mayar da hankali kan sake fasalin tattalin arzikin Najeriya.
A ƙarshe, shugaban ƙungiyar NIDO China, Dr. Oche Barnabas, ya yaba wa Tinubu bisa ƙoƙarinsa na ƙarfafa dangantaka tsakanin Najeriya da China, tare da buƙatar taimakonsa wajen tabbatar da Najeriya a matsayin ƙasar da China ke ɗauka a mai amfani da harshen Ingilishi na asali.