Reshen Kungiyar Malaman Jami’a na Jami’ar Bayero da ke Kano, BUK ya aiyana ranar Litinin, 7 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da ba za ai karatu ba a jami’ar.
Jaridar DailyTrust ta rawaito cewa, kungiyar za tai amfani da ranar domin wayar da kan dalibai, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki kan sabanin da ke tasowa da ya samo asali daga gazawar gwamnati na cika alkawuran da ta yi ga kungiyar tsawon lokaci.
A shekarar 2020 ne dai, ASUU ta tsunduma yajin aiki har na tsawon watanni 10, wanda ta janye a watan Disambar wannan shekarar, bayan an samu yarjejeniya da gwamnatin tarayya.
Tun wancan lokacin kawo yanzu, kungiyar na cigaba da kalubalantar gwamnati na gaza cika alkawura da yarjejeniyar da aka cimma.
Ana dai cikin fargabar cewa, akwai yiwuwar kungiyar ta ASUU ta kara tsunduma yajin aikin a ‘yan kwanaki masu zuwa, matukar ba ta samu tabbatacciyar magana daga bangaren gwamnati ba.