Tsohon Gwmnan jihar Jigawa, Sule Lamido, `ya ce halin da ake ciki yanzu haka a Najeriya a ya samo asali ne daga karerayin da aka yiwa ‘yan kasa yayin yakin neman zabe.
“Wannan ita ce matsalar, al’adar fadin karya ga na kasa, saboda lokacin da ka dandana musu zuma, sannan kuma ka kasa cika musu alkawuran da kai musu – tabbas za a fuskanci matsala. Duk abubuwan da ke faruwar nan saboda karerayi ne da sunan yakin neman zabe.”
Tsohon Gwamnan ya yi wannan maganar ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a daren jiya.
Ya ce akwai abun mamaki a ce, jam’iyyar da dankararta ya kasance tsohon shugaban kasa, tsohon ministan mai, wadda kuma a cikinta akwai tsofin gwamnoni, tsofin sanatoci, tsofin ministoci amma a ce wai ba su san Najeriyar haka take ba.
Ya kara da cewa; “a shugabanci, jahilci ba zai zama uzuri ba, idan ba ka sani ba to kawai kar ka shige shi.”
Da yake Magana kan abin da zai yi in shine shugaban kasa, Sule Lamido ya ce akwai bukatar a sami gudunmawar tunani daga ‘yan kasa, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
“Mu zauna gaba daya. Ina tsofin shugabanni, ‘yan siyasa, jam’iyyu, masu wa’azi, malamai – ku zo. Zan musu bayanin cewa wannan ita ce Najeriya. Kasar da take a rarrabe, babu tausayin juna, kasar da muka mance da ita muna neman biyan bukatunmu . . . wannan ita ce Najeriya, jagorar bakar fata, mai mutane miliyan dari biyu, wadda Allah yaiwa baiwar arziki kowanne iri – me yasa muke cikin wannan yanayin, me ye matsalar? Mu tattauna, mu yi muhawara, kuma mu sa gaskiya tsakanin duk rarrabe-rarraben da ake da su.”
“Magana ce ta mu sa kasar a zuciyarmu sama da komai. Lokacin da muka sa kasar a zuciya sannan ne za mu fara dawo da abun nan da ake kira yarda wadda ta bace. Saboda mutane sun dena yarda da junansu, tsakanin iyali, tsakanin da da uba, tsakanin abokai, tsakanin al’ummu, tsakanin Arewa da Kudu, Gabas da Yamma.”
Sule Lamido ya bayyana abin da yake gani a matsayin matsalar Najeriya; “matsalar kasar nan ita ce, shugabanni ba su da gaskiya, babu wani abu na adalci a yanayin yanda ake gudanar da Najeriya – muna kallon Najeriyar ne a matsayin lokaci na ne, dan bangare na ne, ko kabila ta ce.”
A bayaninsa kan tsarkake hanyar neman amincewar mutane yayin yakin neman zabe ya ce “lokacin da kake so ka samu mulkin siyasa, hanyar ya kamata ta zama mai kyau, mai kunshe da gaskiya – shugaba ya kamata ya ce; ina son na yi jagoranci ne saboda zan yi kaza da kaza, amma kar ya fadi karya ya kuma ci zarafin wasu.”
Sule Lamido ya musanta batun da ake na cewa jam’iyyar PDP ta fadi zabe a 2015 inda ya ce a wannan lokacin Najeriya ce ta fadi ba PDP ba.