For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

A Watanni 12 Kacal, Najeriya Ta Yi Asarar Naira Tiriliyan 2.3 A Satar Danyen Mai

Najeriya ta yi asarar damar fitarwa da siyar da danyen mai kimanin ganga miliyan 65,700,000 a shekara daya da ta gabata saboda lalata bututun mai da yake jawo sace danyen man.

Wannan adadi na gangunan da aka sace, ya sanya Najeriya ta yi asarar kudin shiga kimanin naira tiriliyan 2 da biliyan 300 idan akai amfani da yanayin canjin dala da kuma farashin man a halin yanzu.

Shugaban Kamfanonin Shell a Najeriya, Dr. Osagie Okunbor ya ce, a taron da aka kammala a Abuja kwanannan an bayyana cewa, ganga dubu 180 a kullum da aka kayyade domin Trans Niger Pipeline ya kasance a rufe sama da shekara guda – daga watan Maris 2022 zuwa watan Maris 2023.

Asarar da akai daga watan Maris na bara zuwa watan Maris na bana ya nuna cewa an yi asarar ganga miliyan 65 da dubu 700.

Kudin danyen mai na Brent irin wanda Najeriya ke fitarwa yana tsakanin dala 83 kan kowacce ganga a lokacin da akai asarar, abin da ke nuni da cewa, Najeriya ta yi asarar kudi kimanin naira tiriliyan 2 da biliyan dubu 300 a watanni sha-biyun.

Wannan matsala ta satar danyen mai a Najeriya na jawo tasgaro ga adadin man da Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur, OPEC ta Amincewa Najeriya fitarwa a duk rana.

Okunbor ya kuma bayar da shawara ga sabuwar gwamnati mai shirin fara aiki da ta bayar da fifiko a bangaren tsaron injina da bututan mai.

Comments
Loading...