A ranar Larabar jiya ne dai Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya miƙa ragamar mulkin Jihar Kano ga Mataimakinsa, Dr. Nasiru Umar Gawuna wanda yanzu zai kula da jihar a matsayin muƙaddashin gwamna.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da hakan a sanarwar da ya bai wa manema labarai a ranar Laraba, inda ya ƙara da cewa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tashi zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa domin halartar taron bunkasa sanya hannun jari wanda Kungiyar Gwamnonin Najeriya ke da hannu wajen shiryawa.
Ya ce a yanzu haka, Mataimakin Gwamnan an ba shi damar gudanar da dukkanin aiyuka kafin dawowar gwamnan zuwa Kano.
Bayanin ya kuma umarci duk Kwamishinoni, shugabannin ma’aikatu da sassa, manyan muƙarraban gwamnati, ƴan kasuwa da masu kamfanoni da ma sauran daidaikun jama’a da su baiwa muƙaddashin gwamnan hadin kai.
Haka kuma sanarwar ta baiyana cewa, al’amuran da suke buƙatar kulawar gwamna, yanzu a tura su zuwa ofishin mataimakin nasa.