For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

A Ƙarshe Dai, Tinubu Ya Tare Villa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Lahadin da ta gabata ya tare a ɗaya daga cikin gidajen da ke Gidan Shugaban Ƙasa, Villa, Abuja, wanda aka fi sani da Gidan Gilas (Glass House).

A baya dai, Shugaban yana zuwa ofis ne domin yin aiki a kullum daga gidansa da ya mallaka da ke Asokoro, saboda gyaran gidan Villa da ake yi tun daga ranar da ya karɓi mulki.

Jaridar DAILY TRUST dai ta rawaito cewar, zata yiwu Tinubu ya canza shawara ya tare a Villa a watan Satumba saboda matsin lamba da yake samu daga ƴan ƙasa.

Gidan Gilas dai yana gefen Fadar Shugaban Ƙasa a cikin Villa, an kuma tanade shi saboda ya kasance gida mafi daraja na sauƙar baƙin shugaban ƙasa.

Comments
Loading...