Gwamnonin Jam’iyyar APC sun saɓawa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a wajen fitar da waɗanda zasu jagoranci jam’iyyar APC a matakin ƙasa, inda suka zubar da mutane huɗu cikin mutane biyar da Shugaba Buharin ya bayar.
Sai dai kuma duk da gwamnonin sun saɓawa buƙatar Shugaba Buharin a mafi yawan sunayen da ya gabatar, tsohon gwamnan Jihar Nassarawa, Sanata Abdullahi Adamu wanda ke saman sunayen ne ya samu nasarar zamewa Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa biyo bayan tabbatar da shi da akai a lokacin taron da aka gudanar a Eagle Square da ke Abuja.
Sanata Abdullahi Adamu ya samu nasarar kasancewa sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ne bayan an sanya sauran abokan hamayyarsa sun janye masa.
A takarda mai shafuka 12 da ta zagaya filin taron kafin farawa, gwamnoni 22 na jam’iyyar sun gabatar da sunayen mutane 78 a matsayin shugabanni na ƙasa da kuma yankuna.
Dukkan gwamnonin ne suka sanyawa takardar hannu, yayin da suka cire sunayen wasu jiga-jigai da Buhari ya gabatar, waɗanda suka haɗa da; tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Sanata Ken Nnamani, tsohon Ɗan Majalissar Wakilai, Farouk Adamu Aliyu, Injiniya Ife Oyedele, da Arch. Waziri Bulama.
Tun da farko dai Shugaba Buhari ya buƙaci a baiwa mutanen muƙaman mataimakin shugaban jam’iyya na yankin Kudu, mataimakin shugaban jam’iyya na yankin Arewa, sakataren jam’iyya na ƙasa da kuma sakataren tsare-tsare na ƙasa.
Bayan gwamnonin sun cire sunayen waɗanda Buharin ya gabatar, sun samu nasarar maye gurbinsu da mutanensu, waɗanda suka haɗa da; Chief Emma Enuekwu, Sanata Abubakar Kyari, Sanata Iyiola Omisore, da kuma Suleiman M. Argungu.
An sanya jiga-jigai huɗun da Buharin ya gabatar sun janyewa waɗanda gwamnonin suka gabatar.
Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ne jagoran kwamitin zaɓen jam’iyyar, kuma shine ya baiyana waɗanda aka tabbatar a matsayin sabin shugabannin jam’iyyar APCn na ƙasa.
(DAILY TRUST)