Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa magance matsalar tallafin mai, da canjin kudaden waje domin a farfado da tattalin arzikin Najeriya zai iya jawowa shugaban kasa mai zuwa rasa damarsa a karo na biyu idan ya nemi zabe.
Duk da haka, gwamnan ya bayyana cewa, kasar nan na bukatar irin wannan shugaban, wanda zai tashi sama da hangen kujerarsa ya dauki tsaurara kuma wajibabbun hukunce-hukunce domin tabbatar da tattalin arzikin kasar ya ci gaba.
El-Rufa’i ya bayyana hakan ne a wajen tattaunawa na kaddamar da World Bank Nigeria Development Update da Country Economic Memorandum a jiya Alhamis a Abuja.
Ya bayyana cewa, tsare-tsaren da suka kamata, da kuma daukar matakai zasu cire kalmar mai yiwuwa (potential) daga kundin kalmomin Najeriya, kuma (Najeriya) a karshe zata zama kasar da ta dace mu kasance a ciki.
“Shugaban kasar Najeriya mai zuwa, dole ne ya zama yana da aniyar yin wa’adi daya kacal idan hakan ya zama dole,” in ji gwamnan a lokacin da yake amsa tambaya kan tallafin man fetur.