For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Abun Da Zan Yi Idan Na Ci Zaben Shugaban Kasa A 2023 – Peter Obi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi ya bayyana cewa zai rage matsalar tsaro da talauci a Najeriya idan har ya ci zaben shugaban kasa a shekarar 2023.

Tshohon Gwamnan Jihar Anambra, ya bayyana cewa yana tsammanin samun cimma nasarar yin hakan ne ta hanyar kirkirar aiyukan yi da kuma kawo ingantaccen sauyi a bangaren sanya hannun jari.

Ya kuma yi alkawarin cewa zai sauya tattalin arzikin Najeriya daga mai lakume kudade zuwa mai samar da kudade.

Peter Obi ya bayyana hakan ne a wasu rubuce-rubuce da ya fitar a shafinsa na Twitter a yau Alhamis biyo bayan walimar da ya gudanar da wasu matasan Najeriya.

Ya rubuta cewa, “Bayan mun ci zaben shekarar 2023, mun yi shirin amfani da hanyoyin samar da aiyukan yi da sanya hannun jari domin a hankali, mu rage yawan faruwar matsalar tsaro da kuma talauci, a lokaci guda kuma mu ciyar da tattalin arziki gaba daga mai lakume kudade zuwa mai samar da kudade.

“Tabbas ne, babbar matsalar da muke fuskanta baya da rashin ingantaccen shugabanci, shine rashin hadin kan manya. Amma kuma, kar mu manta da nasihar Dante Alighieri da yake cewa ‘Guri mafi zafi a jahannama, an tanade shi ne domin wadanda suke kin yin komai a lokacin da ake cikin kakanikayi,” in ji Peter Obi.

Comments
Loading...