Ƙungiyar Afenifere ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da neman koma wa salon mulkin kama-karya irin na Janar Sani Abacha.
Ƙungiyar ta bayyana shirinta na kafa wata ƙungiyar siyasa don ƙwace mulki daga hannun gwamnati mai ci a zaben 2027.
Sakataren Yaɗa Labarai na Afenifere, Justice Faloye, ya yi wannan tsokaci ne a wata hira da aka yi da shi a wata kafar talabijin a Lagos.
Faloye ya bayyana mulkin Tinubu tun bayan hawansa kan mulki a shekarar 2023 a matsayin gazawa mai girma, inda yake cin zarafin wadanda suka saɓa masa a ra’ayi.
Ya ƙara da cewa gwamnatin na cin mutuncin shugaban ƙungiyar ƙwadago da kuma tsare mutane saboda shiga zanga-zangar ƙin jinin yunwar da gwamnatin Tinubu da jawowa ƴan Najeriya.
Faloye ya yi zargin cewa an hana ƴancin zanga-zanga a ƙarƙashin mulkin Tinubu, inda masu zanga-zanga suke fuskantar tsarewa ba bisa ƙa’ida ba.
Har ila yau, ya ce al’ummomin duniya sun yi Allah wadai da mulkin Tinubu bisa zargin kama mutanen da ke yin zanga-zanga cikin lumana a cikin tsarin dimokaraɗiyya.
Afenifere ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya saurari shawarar Farfesa Wole Soyinka kan gujewa kama-karya a Najeriya.
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa, idan ba a ɗauki mataki ba, Najeriya na iya komawa zamanin kama-karya irin na mulkin soja.
A ƙarshe, Faloye ya bayyana cewa Afenifere na duba yiwuwar kafa wata jam’iyyar siyasa don tabbatar da gaskiya da adalci a Najeriya.