An Cire ‘Yan Mata Daga Jerin Masu Komawa Makarantun Sakandare A Afghanistan
‘Yan Taliban sun cire’ yan mata daga makarantun sakandare na Afganistan, bayan da suka ba da umarnin cewa samari da malamai maza ne kawai za su koma aji.
Wata sanarwa daga kungiyar masu kishin Islama ta ce za a ci gaba da karatun sakandare said ai sanarwar ba ta ambaci ‘yan mata ko mata ba.
Wata ‘yar makaranta a Afganistan ta shaidawa BBC cewa abin ya ba ta haushi. Tace “komai ya zama duhu sosai.”
Duk da cewa Taliban ta yi alkawari na kawo sauyi to amma wannan ita ce sabuwar alama da ke nuna cewa kasar Afganistan na komawa kan madafun iko irin na shekarun 1990.
A wani labarin kuma, a ranar Juma’a ‘yan Taliban sun rufe ma’aikatar harkokin mata tare da maye gurbin ta da sashen da ya taba aiwatar da tsauraran koyarwar addini.
A lokacin mulkin Taliban tsakanin 1996 zuwa 2001, Ma’aikatar Yada Adalci da Kare Gurbacewa ita ce ke da alhakin tura abin da ake kira ‘yan sandan tabbatar da da’a kan tituna don aiwatar da tsauraran fassarar dokokin addinin Musulunci.
Wata sanarwa da aka fitar gabanin bude makarantun a Afghanistan ranar Asabar ta ce: “Duk malamai maza da dalibai maza su halarci guraren karatun su.”
Makarantun sakandare a kasar galibi na daliban da ke tsakanin shekaru 13 zuwa 18. Yawancin makarantun ma ba a hada maza, wanda hakan zai sa Taliban ta rufe makarantun ‘yan mata cikin sauki.
”Na damu matuka game da makomata, ” in ji wata ‘yar makarantar Afganistan, wacce ta ke da burin zama lauya.
“Komai ya yi duhu sosai. Kowace rana ina farkawa ina tambayar kaina dalilin da ya sa nake raye? Shin ya kamata in zauna a gida in jira wani ya kwankwasa kofa ya ce in aure shi? Wannan ita ce kadai manufar zama mace?”
Mahaifinta ya ce: “Mahaifiyata ba ta iya karatu da rubutu ba, kuma mahaifina kullum yana zagin ta yana kiran ta da wawa. Ba na son ‘yata ta zama kamar mahaifiyata.”
Wata ‘yar makaranta,’ yar shekara 16 daga Birnin Kabul, ta ce “wannan ranar bakin ciki ce”.
“Ina son zama likita! Kuma wannan mafarkin ya bace. Ba na tsammanin za su bar mu mu koma makaranta. Ko da za su sake bude manyan makarantun, ba sa son mata su zama masu ilimi.”
A farkon makon nan, kungiyar Taliban ta sanar da cewa za a bar mata su yi karatu a jami’o’i, amma ba za su iya yin hakan tare da maza a hade ba kuma za su yarda da sabuwar dokar sanya sutura.
Wasu na ganin sabbin dokokin za su ware mata daga neman ilimi saboda jami’o’in ba su da wadatar da za su ba da azuzuwa daban-daban.
Haka kuma, hana ‘yan mata daga makarantun sakandare na nufin babu wanda zai sami damar ci gaba zuwa karin ilimia jami’o’i cikin matan.
Tun lokacin da aka cire hambare Taliban daga mulki a 2001, an samu gagarumin cigaba wajen inganta harkar ilimi da cigaban karatu a Afghanistan – musamman ga ‘yan mata da mata.
Adadin ‘yan mata a makarantun firamare ya karu daga kusan sifili zuwa miliyan 2.5, yayin da yawan karatun mata ya ninka ninki biyu cikin shekaru goma zuwa kashi 30%.