Bulaliyar Majalissar Dattawa, Orji Uzor Kalu ya ce, samuwar Ahmad Lawan a matsayin dan takarar Shugaban Kasa na maslaha zabin mafiya mambobin Kwamitin Shugabancin Jam’iyya na Kasa, NWC, ne, domin kuwa Abdullahi Adamu ba shi da karfin shi kadai ya iya daukar wannan matsaya.
Kalu ya fadi haka ne a wata tattaunawa ta talabijin a jiya Litinin, inda yake mayar da martani kan masu kalubalantar kasancewar Ahmad Lawan a matsayin dan takara na maslaha.
Ya ce, ba zai taba yiwuwa ba, Abdullahi Adamu ya dauki wannan hukuncin ba tare da samun goyon bayan Shugaban Kasa Buhari ba.
Ya kara da cewa, cikin shugabannin jam’iyya 23 da suka hadu domin fitar da matsayar, iya mutum biyu ne suka nuna rashin yardarsu.
Ya baiyana Ahmad Lawan a matsayin mafi cancanta da kuma dacewa a cikin dukkanin sauran ‘yan takarar da ke neman a tsayar da su.