Kungiyar Al’ummar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, ta yi watsi da takarar Shugaban Majalissar Dattawa, Ahmad Lawan, a matsayin dan takarar maslaha na jam’iyyar APC a babban zaben shekarar 2023.
Kungiyar ta yi zargin cewa, baiwa Ahmad Lawan takarar Shugaban Kasa zai zame matsala ne ga jam’iyya mai mulki a zabukan shekarar 2023.
Ohanaeze, saboda haka, ta gargadi shugabancin jam’iyyar da ya sake duba hukuncin tsayar da Ahmad Lawan, inda ta ce, Ahmad Lawan ba shi da karbuwa a fadin kasa, da kuma nagartar da zai iya kayar da dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
TASKAR YANCI ta rawaito dai a baya cewa, Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya aiyana Shugaban Majalissar Dattawa, Ahmad Lawan a matsayin dan takarar da aka amince da a matsayin maslaha a jam’iyyar APC.
To sai dai kuma, gwamnonin jam’iyyar APC, sun fito sun kalubalanci hakan, inda suka matsa cewar dole ne takara ta koma yankin Kudu a zaben shekarar 2023.