Rahoton watan Mayu kan cin zarafin mata na Cibiyar CITAD ya nuna cewa, ba a samu aikata fyaɗe ko guda ɗaya ba a watan, sai dai kuma an samu ƙaruwar cin zarafin mata da kaso 150% a jihar.
Jami’in kula da sashin Cin Zarafin Mata na CITAD, Buhari Abba ne ya sanar da hakan ga ƴanjarida.
Ya ce an samu raguwar aikata fyaɗen ne saboda wayar da kan mutane da ake yi, wanda hakan ta sa yanzu ana iya kai ƙorafin fyaɗe da sauran cin zarafi ta hanyar manhajar GBV wadda aka tanada domin hakan.
Buhari Abba ya ce, “Idan aka kwatanta da bayanan da aka samu a watannin baya, har yanzu ana samun ƙaruwar cin zarafin mata. An turo mana ƙorafe-ƙorafe 85 ta hanyar manhajar GBV a wannan watan, waɗanda suka haɗa da neman yin lalata, cin zarafi ta yanar gizo, da dukan mata”.
Ya kuma ce, manhajar GBV zata samu nasara ne kaɗai idan har masu ruwa da tsaki sun ƙyale ta ta samu.
Da yake kira ga iyaye, ƴan-uwa da masu ɗaukar nauyi wajen cewa, a ko da yaushe da su rinƙa sanar da cin zarafi ta GBV ga hukumomin da suka dace, ya kuma yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da dokokin da za hukunta masu aikata cin zarafi da su.