For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

“Akwai Bukatar PDP Ta Dawo Mulki”, In Ji Okowa A Jawabin Karbar Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

Gwamna Ifeanyi Okowa ya godewa Atiku Abubakar bisa zabarsa a matsayin dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa, inda ya ce akwai bukatar jam’iyyar PDP ta dawo mulki.

Gwamna Okowa na Jihar Delta ya bayyana hakan ne a yau Alhamis lokacin da yake jawabin karbar takarar Mataimakin Shugaban Kasa a takarar Shugaban Kasa da Atiku Abubakar yake yi a jam’iyyar PDP.

“Bayan na gode maka, rankaidade, na fuskanci cewa akwai babban aiki a gabanmu, amma na sani cewa, Allah ya tsara hakan, kuma da temakonsa, dukkaninmu zamu yi aiki tukuru domin tabbatar da samun nasara ga jam’iyyarmu”, in ji Okowa a yayin jawabin.

Okowa, ya bayyana cewa akwai gagarumin aiki a gaban ‘yan jam’iyyar, indai yai kira da su yi aiki tare.

“Babu shakka akwai gagarumin aiki a gaban kowannenmu. Hanyar sake gini zai zama aikin gamayya ne, kuma mun yarda cewar zasu so kasancewa cikin wannan gwagwarmayar kafa sabon tarihi a karshen lamari,” in ji shi.

Okowa wanda yai wannan jawabi ‘yan awanni bayan Atiku ya zabe shi a matsayin mai mara masa baya a takara, zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu a matsayin gwamnan Jihar Delta a shekara mai zuwa.

Tun a farko dai, Atiku ya yi bayanin cewa ya zabi tsohon dan Majalissar Dattawan ne bayan tuntubar jagororin jam’iyyar.

Atikun ya ce, an nada kwamiti na musamman domin su temaka masa wajen zabin daya daga cikin mutane ukun da aka gabatar masa, wanda a karshe ya zabi Gwamnan na Jihar Delta.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, ya kuma ce, ya zabo wanda yake da kwarewa, da kuma fahimta, kuma wanda zai iya temakawa wajen samar da mafita ga matsalolin da suke addabar Najeriya.

Comments
Loading...