Akwai wani dan Majalisar Tarayya cikin manyan mutanen da ke daukar nauyin shugabannin kungiyoyin da ke kira a raba kasar Najeriya, in ji Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma’a.
Amma, bai bayyana ko wanene dan majalisar ba, haka kuma bai fadi daga wacce majalissar ya fito ba cikin majalissu 2 na Najeriya – Majalisar Wakilai ko Majalisar Dattawa.
“Kamen da aka yi kwanan nan na Nnamdi Kanu da Sunday Adeyemo, da kuma binciken da ake yi yanzu ya nuna wasu manyan masu kudi na temakawa wadannan mutane,” Shugaban ya fada a jawabinsa ga al’ummar kasar don tunawa da cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yancin kai.
“Muna bin diddigin wadannan masu kudi, ciki har da wanda aka bayyana a matsayin memba na Majalisar Dokoki ta Kasa.”
Yayin da Kanu ke jagorantar haramtacciyar kungiyar Indigenous People Of Biafra (IPOB), Adeyemo – wanda aka fi sani da Sunday Igboho, mai neman kasar Yarabawa ne.
Mutanen biyu sun tsere daga kasar bayan samamen da jami’an tsaro suka kai gidajensu da kuma gurfanar da su da gwamnati ta yi.
An kama Kanu, inda aka dawo da shi kasar a watan Yuni, shekaru hudu bayan ya tsere daga kasar sakamakon abin da ya ce ya mamaye gidansa da ke Afara-Ukwu, kusa da Umuahia, babban birnin jihar Abia.
Shi kuwa Igboho, ya tsere zuwa Jamhuriyar Benin makwabciyarsa a watan Yuli bayan da aka kai samame gidansa da ke Ibadan, Jihar Oyo.
Daga baya hukumomin Benin sun cafke shi a kan hanyarsa ta zuwa Jamus, kuma ana ci gaba da fafutukar taso keyarsa don sanin makomarsa.