Akwai alamun cewa, mambobin Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, sun kammala yanke hukunci kan kara wa’adin yajin aikin da suke yi da wata biyu.
A safiyar yau Litinin ne, wani jigo a shugabancin kungiyar na kasa ya sanar da jaridar DAILY TRUST cewa, kungiyar ta kammala shirin cigaba da yajin aikin har na tsawon sati takwas, domin cigaba da matsawa Gwamnatin Tarayya kan bukatun kungiyar.
“Zan iya fada muku cewa, ana cigaba da tattaunawa kan yajin aikin gargadi da muke yi, amma akwai yiwuwar mu kara turashi zuwa nan da sati takwas”, in ji shugaban wanda ya bukaci a boye sunansa.
To amma lokacin da aka tuntubi Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya baiyana maganar kara wa’adin yajin aikin a matsayin jita-jita, inda ya kara da cewa har yanzu mambobin kungiyar na cigaba da tattaunawa kan mataki na gaba da zasu dauka.
“Ba mu yiwa ‘yan jarida wannan bayanin ba. Kawai dai jita-jita ce. Har yanzu tattaunawa tana ci gaba da gudana a yanzu haka da nake magana da ku,” in ji
Farfesa Osodeke yayin tattaunawa da DAILY TRUST.
A wani bangaren kuma, wani rubutu a shafin Twitter na ASUU wanda ba a tantance ba, ya nuna cewa, kungiyar ta kara wa’adin yajin aikin gargadin da sati takwas.