For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Akwai Yiwuwar Buhari Ya Sake Tsige Wasu Ministocin

Akwai yiwuwar Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya sake tsige wasu ministocinsa bayan sauraron irin kokarin da kowanne minister yai wajen tabbatuwar kudire-kudire 9 na gwamnatinsa.

Shugaban ya nuni da hakan ne a lokacin bude taron tantance kokarin ma’aikatu na tsakiyar zango wanda aka shirya domin binciken irin nasarar da aka samu kan cimma kudire-kudire 9 na gwamnatinsa da kuma duba kokarin mukarraban gwamnatin.

Taron tantancewar yana samun halartar ministoci, manyan sakatarori da sauran manyan mukarraban gwamnatin Najeriya.

Shugaba Buhari ya ce zai zauna domin kallo da sauraron duk jawabai kan bayanan kowane bangare domin tantance kokarin gwamnatin tasa cikin shekaru 2.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, a irin wadan nan tarurruka na baya, Shugaban yana halartar bikin budewa ne kawai, inda yake barin sauran masu tantancewa su jagorancin sauran kwanakin taron.

A jawabin da ya gabatar a bude taron na bana, Shugaba Buhari ya gargadi ministocin da manyan sakatarorin da su matukar kula da abubuwan da aka dora musu wajen cimmuwar kudire-kudiren gwamnatinsa.

A karo na farko, a watan Satumban da yagabata ne dai Shugaba Buhari ya tsige Ministan Harkokin Noma, Sabo Nanono da takwaransa Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman saboda dalilai na rashin yin aiki yanda ya kamata.

Comments
Loading...