Alamu sun nuna cewa, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC za ta iya tura gudanar da zabubbukan shekarar 2023 gaba da yanda ta ambata a baya.
Wannan kuwa zai faru ne, idan har Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya haura ranar Talata, 22 ga watan Fabrairu, 2022 bai sanyawa sabuwar dokar zabe hannu ba.
‘Yan makonni kadan ne da kammala zaben shekarar 2019, INEC ta fitar da sanarwar jadawalin gudanar da zaben shekarar 2023.
A jadawalin, INEC ta baiyana cewar za a gudanar da zaben Shugaban Kasa da na ‘Yan Majalissar Tarayya a ranar 18 ga watan Fabrairu na shekarar 2023.
To sai dai kuma, kusan shekara guda ya rage kafin zuwan wannan rana, INEC ba ta fitar da jadawalin yanda za ta shiryawa zaben ba, a cewarta, tana jiran sanya hannun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kan Kudirin Dokar Zabe wanda aka yiwa gyara.
Sashi na 28(1) na Kudirin Dokar Zabe ta 2022 ya nuna cewa, ana bukatar INEC ta sanar da fara shiryawa zabe kar ya gaza kwanaki 360 kafin ranar da za a gudanar da zaben.
Rahotanni sun nuna cewa, wa’adi na karshe da INEC take da shi na fitar da jadawalin shiryawa zaben shine ranar Talata, 22 ga watan Fabrairu, 2022, idan har za a tabbatar da ranar 18 ga watan Fabrairun badi a matsayin ranar zaben Shugaban Kasa da na ‘yan Majalissar Tarayya.