Farashin ɗanyen mai ya tashi a duniya inda aka siyar da shi kan dala 84 a kan kowacce ganga, abin da ya jawo tunanin ƙaruwar farashin man fetur a Najeriya a kwanaki masu zuwa.
Ɗanyen mai, wanda shine ƴar manuniya kan yanda farashin albarkatun mai zasu kasance a duniya, ya kasance tsakanin dala 75 da dala 78 kan kowacce ganga a tsawon wata guda, to sai dai kuma ya fara tashi tun daga makon da ya gabata.
Dillalan mai sun bayyanawa wakilin PUNCH cewa, ƙaruwar farashin ɗanyen mai hadi da raguwar darajar naira zai jawo ƙaruwar farashin man fetur ga ƴan Najeriya, duba da cewar, Kampanin Dillancin Mai na Ƙasa, NNPCL yana kan bakarsa ta siyar da fetur a yanda kasuwa tai nuni.
Labari Mai Alaƙa: CIRE TALLAFI: Ma’aikata Zasu Tsunduma Yajin Aiki Ranar Laraba Mai Zuwa A Najeriya
Haka kuma, duk da a yanzu wasu dillalan man sun fara shigo da man fetur Najeriya baya da NNPCL, amma har yanzu dai NNPCL ne mafi shigo da man da ƴan Najeriya ke siya.
Sakataren Ƙungiyar Dillalan Man Fetur Masu Zaman Kansu, Mohammed Shuaibu ya bayyana cewa, tashin farashin ɗanyen mai da raguwar darajar kuɗi dole ne su jawo ƙaruwar farashin man fetur tun da an ƙyale kasuwa tai halinta.
Babban Jami’in Sadarwa na NNPCL, Garba-Deen Mohammad ya jaddada cewa, tun da an cire tallafin man fetur, kamfaninsu zai tsaya a matsayarsa ta siyar da mai a kan farashin da kasuwa ta nuna, inda ya ƙara da cewa, da gwamnati ce ke shan wahalar biyan tallafin.
