For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Akwai Yiwuwar Samun Hadari Da Tsawa A Wasu Sassa Na Najeriya, Juma’a Zuwa Lahadi – NIMET

Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya NIMET, ta fitar da hasashen cewa za a samu zafin rana da kuma tsawa a ranakun Juma’a, Asabar da kuma Lahadi a wasu sassa na Najeriya.

Wannan ya fito ne a bayanin hasashen yanayin da ta fitar ranar Alhamis a Abuja.

Hukumar ta ce za a kwalla rana a yankin Arewa a ranar Juma’a da kuma yiwuwar samun tsawa a wasu yankunan na Taraba a safiyar Juma’ar.

“Hadari zai yi ta haduwa, rana za ta dinga fitowa jifa-jifa a yankin Arewa ta Tsakiya tare da yin tsawa a wasu yankunan jihohin Filato da Nasarawa da Naija da Binuwai da kuma Abuja da rana da kuma yamma,” a cewar NIMET.

Ta kara da cewa, “Hadari zai yi ta haduwa a biranen da ke kusa da gabar teku amma ba za a yi tsawa ba a jihohin Ogun da Akwa Ibom a safiyar.”

“Da rana kuma ana sa ran za a yi ta tsawa a wasu yankunan jihohin Imo da Abia da Ebonyi da Osun da Lagos da Rivers da Bayelsa da Delta da Cross River da kuma Akwa Ibom,” in ji hukumar.

NIMET ta kuma ce akwai hasashen za a kwalla rana a Arewa tare da yiwuwar yin tsawa da safe a yankunan jihohin Adamawa da Taraba da Borno da Yobe da kuma Jigawa ranar Asabar.

Sannan za a yi tsawa a biranen Kano da Kaduna da Katsina da Zamfara da Sokoto da Kebbi da Bauchi da rana da kuma yamma a ranar Asabar.

Comments
Loading...