For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Al’adar Siyan Kuri’a Ta Mamaye Zaben Annabara

Bayanan da suka fito daga Gamayyar Kungiyoyin Cigaban Al’umma sun nuna cewa, zaben gwamnan jihar Annabara da ya gabata an yi cikin zaman lafiya amma kuma siyan kuri’au ya mamaye zaben.

A rahoton da gamayyar ta fitar ranar Lahadi game da zaben, Gamayyar ta bayyana wadansu bayanai da suka danganci siyan kuri’u da suka hada da siyar da kuri’u kan kudi tsakanin Naira 1000 da Naira 6000 a gurare daban-daban.

Gamayyar ta kuma gano cewa, an aiwatar da cinikin kuri’un a boye a wasu guraren, in da a wasu guraren kuma aka yi kiri-kiri a bainar jama’a ba tare da tsoron jami’an tsaro.

Haka kuma gamayyar kungiyoyin sun bayyana cewa a kwai wani akwatin zabe da masu zabe a akwatin suka ki karbar Naira 5000 da akai nufin ba su domin su kada kuri’a, inda gamayyar ta yaba da halin mutanen akwatin.

Gamayyar ta kuma gano cewa, ma’aikatan wucin gadi na Hukumar Zabe mai Zaman Kanta da kayan zabe sun isa mazabu a makare kamar yanda masu duba zaben daga bangaren gamayyar suka bayyana.

Haka kuma an gano cewa an samu yawaitar rashin aiki na na’urar tantance masu zabe Bimodal Verification Accreditation System (BVAS), inda ta kasa tantance hoton yatsun masu zabe da kuma kasa tantance fuskokinsu.

“Wannan matsala ta faru a kaso 59% na akwatinan zaben, inda kuma ake samun akalla mintina 5 a kaso 65.8% na akwatinan zaben.

“Haka kuma, wadansu ma’aikatan sun fuskanci matsaloli wajen iya aiki da na’urorin tantance masu zabe. A wasu mazabun kuma na’urorin na aiki amma babu sauri, inda ake daukar mintuna 10 kafin a tantance mai kada kuri’a,” in ji gamyyar.

Duk da matsalolin da aka samu a zaben na jihar Anambara, akwai abubuwa masu kyau da suka faru.

Gamayyar Kungiyoyin ta bayyana cewa an samu fitar masu kada kuri’a sama da yanda akai tsammani.

Haka kuma ma’aikatan zabe sun ba da muhimmanci ga masu bukata ta musamman, mata masu ciki da kuma tsofi wajen yin zabe da wuri a akwatinan zabe da dama.

A wasu mazabun kuma irin wadannan kalolin mutane kuma ba su sami damar yin zaben ba.

Comments
Loading...